Prince Philip: Rayuwar mijin Sarauniya cikin hotuna

Duke of Edinburgh, 1977
Bayanan hoto,

Duke na Edingburgh an haife shi a tsibirin Girka na Corfu ranar 10 ga Yunin 1921. Salsalar zuri'arsa ta tattaro zuri'ar iyalan gidan sarautar na Denmark, da Jamus da Russia da Birtaniya.

White Line 1 Pixel

Asalin hoton, Getty Images / Alamy

Bayanan hoto,

Yarima Philip shi ne da daya kwal ga Yarima Andrew na kasar Giris da Gimbiya Alice ta Battenberg.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yarima ya fara karatunsa a kasar Faransa a makarantar Amurkawa ta Maclannet American School da ke St. Cloud, kuma ana iya gnainsa tare da abokan karatunsa.. Tun yana dan shekara bakwai ya koma ingila, inda ya zauna tare da danginsa zuri'ar Mountbatten da ke Ingila, inda ya rika halarta makarantar yamma ta Surrey.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Daga bisani ya halarci makarantar kwana ta Gordonstoun, wadda mashahuri masani a fagen ilimi Kurt Hahn ya kafa a Arewacin Scotland, inda ya shahara a harkar wasanni.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

A zamanin yakin Duniya na biyu, Yarima Philip ya kasance dalibi mai samun horon jan ragamar jirgin ruwan yaki, inda ya yi aiki a jirgin ruwan yaki na HMS Valian. Lokacin da aka tare jirgin ruwan yakin Italiya a kasar Girka cikin shekarar 1941, Philip ya bayar da umarnin baza hasken hange-hange, har ta kai ga ya hasko

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

A hukumance aka sanar da baikonsa da Gaimbiya Elizabeth cikin watan Yulin 1947....

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

... sannan suka yi aure a ranar 20 ga Nuwambar wannan shekarar.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Ana iya ganin Yarima a nan yana wasan kwallon Polo a wajen shakatawa na Cowdray Park, inda ya kai ga wasan kusa da karshe na cikin kofin Roehamptom. Ya kasance daya daga jiga-jigan 'yan wasan Polo a kasar Birtaniya.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Basarake Duke ya kasance mai matukar son wasan kwallon Cricket. A nan kungiyarsa, ta hado da tsofaffin fitattun 'yan wasan Ingila, inda suka yi wa Kyaftin guda kawanya, wato Duke na Norfolk.

Bayanan hoto,

Duke da Sarauniya sun haifi 'ya'ya hudu, (daga hagu) akwai Edward da Andrew da Anne da Charles, a hoton da aka dauka cikin shekarun 1960.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Ana iya ganin ma'auratan lokacin da suka kai ziyara wata gona a katafaren gidansu na Balmoral, don murnar bikin cikarta shekara 25 da aure.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

A shekarar 1977 Yarima ya yi wa Sarauniya rakiya lokacin da take bikinta na cika shekara 25 a karagar mulki. Ana iya ganinsu sanye da tufafin da aka saka da fatar Maori Kahu-Kiwi a wajen shakatawa na Rubgy da ke Gisborne, da ke Arewacin tsibirin kasar New Zealand, lokacin da suka halarci bikin sarautar New Zealand na Polynesian Festival a Fabrairu.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Daga bisani cikin wannan shekarar dai ma'auratan 'yan sarauta sun rika daga wa jama'a hannu yayin da jirgin ruwan Concorde ya wuce a guje ta gaban jirgin ruwan sarautar Birtaniya na 'Royal Yacht Britannia.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

A Agustar 1979 an kashe dan uwan Sarauniya, Lord Louis Mountbatten a harin bom din 'yan tawayen Ireland na IRA da suka kai wa kwale-kwalensa a Ireland. Duke na Edingburgh ya komo Birtaniya bayan da ya samu labarin, bayan da ya kasance a jerin wadanda suka tuka jirgin da ya kai ga gaci a Normandy da ke Arewacin Faransa.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Kare halittu a muhallinsu al'amari ne na sha'awa da ya damfaru tsawon zamani a tattare da Duke na Edingburgh, don haka ya cancanci kasancewa Shugaban Asusun kula da Namun daji na duniya.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

A shekarar 1985 Duke na Edingburgh kewaye da iyalansa, wadanda suka hada da matashi Yarima Williams da Harry, a lokacin da suka taru don kallon shawagin jiragen sama a saman fadar Buckingham, inda rundunar sojojin Birtaniya da na kasashen rainon Birtaniya suka yi atisayen da ake yi wa lakabin 'Trooping the Colour.'

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

A shekarar 1996 Duke ya yi rakiya ga Shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela, lokacin da ya duba faretin sukuwar dawakai ta ban girma a ranar farko da ya kai ziyara kasar Birtaniya.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Yarima Philip ya tallafa wa Sarauniya (a ayyukanta) tsawon shekaru 60 da doriya na jan ragamar mulkinta, al'amarin da ya hada da bikin cikarta a karagar mulki shekara 50, wanda aka gudanar cikin shekarar 2002.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Yarima sanya kyautar karramawa ta Duke na Edingburgh, wadda aka bullo da ita da manufar inganta rayuwar matasa, a shekarar 1956. A nan yana yin barkwanci da wadanda suka samu kyautar karramawa ta Duke na Edingburgh a Holyroodhouse cilkin shekarar 2010.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Duke ya ci gaba da shiga gasar wasanni har da tsufansa, al'amarin da ya hada da gasar tuka keken dawaki ta Sandringham cikin shekarar 2005.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dubban mutane ne suka yi dandazo a wajen fadar Buckingham don su gaishe da iyalan gidan sarauta bayan auren jikan Yarima Philip, Yarima William da aka yi da Catherine Middleton a shekarar 2011.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Watanni sha biyu daga bisani, Yarima ya kasance cikin koshin lafiya lokacin da ya raka Sarauniya taron tambarin sarauta a jirgin ruwan alfarma da kasaita, al'amarin da ya haifar da jikewarsu a ruwa lokacin bikin cikar Sarauniya shekara 60 a karagar mulki da ta gudanar a kogin pageant ranar 3 ga Yunin 2012. Shi da Sarauniya sun tsaya tsaye kyam har tsawon mintuna 80 ana tafiya, yayin da kananan jiragen ruwa dubu suka yi musu rakiya har tsawon mil bakwai daga Kogin Thames zuwa tulluwar gada. Sai dai Duke ya yi jinya a asibiti, inda ya yi fama da ciwon mara kafin bikin cika shekara 60 a karaga da aka gudanar ranar 4 ga Yuni.

Asalin hoton, Alex Livesey / Getty Images

Bayanan hoto,

Bayan da ya murmure, ya samu cikakken koshin lafiyar da ya iya raka Gimbiya Anne ta kalli wasan tseren sukuwar dawaki na kasar Birtaniya, wadanda suka hada da jikarsa Zara Philips, wadda ta yi gasarta a yammacin gasar Olymfik din shekarar 2012.

Asalin hoton, Jack Hill/The Times/PA

Bayanan hoto,

A Yunin 2013 Duke ya halarci ibada a majami'ar Westminster Abbey don murnar zagayowar cikar Sarauniya shekara 60 da hawa gadon sarauta.

Asalin hoton, Brian Lawless / PA

Bayanan hoto,

A shekarar 2014 ya yi wa Sarauniya rakiya a rangadin da ta kai Arewacin Ireland. An dauke shi a hoto yana sa hannu a littafin masu kawo ziyara gidan sarauta na Hillsborough Castle da ke Belfast.

Asalin hoton, Jonathan Brady /PA

Bayanan hoto,

Sarauniya Elizabeth II tare da rakiyar Duke na Edingburgh yayin da take kunna wutar farko kan tsirin kwarkwaro-kwarkwaro sama da 200 a wajen bikin cika shekara 70 da murnar samun nasarar yaki a Turai a gidan sarautar Windsor Castle.

Asalin hoton, Andrew Matthews / PA

Bayanan hoto,

Basarake Duke da dansa Charles suna cikin annashuwa lokacin da suka kai ziyara Poundbury, wajen birni da ke gabar Dorchester, inda Sarauniya ta kaddamar da mutum-mutumin mahaifiyar Sarauniya.

Asalin hoton, Chris Radburn / PA

Bayanan hoto,

A Afrilun 2017 Basarake Duke ya raka matarsa wajen bude Cibiyar kula da giwa a gidan namun daji na ZSL Whipsnade da ke Bedfordshire. Si dai cikin Mayu ya bayar da sanarwar zai dakatar da gudanar da ayyuka a bainar jama'a tun da ya kai shekara 95, tare da cikakken tallafin Sarauniya.

Asalin hoton, Dominic Lipinski / PA

Bayanan hoto,

Sarauniya tare da Duke sun yi dshiru na minti guda a farkon bikin lambun fadar Buckingham da aka gudanar ranar 23 ga Mayun 2017 don tunawa da wadanda aka kashe (ko suka hallaka) a bikin dafdalar Ariana Grande da aka yi a Manchester.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Basarake Duke ya kasance mijin Mai sarautar Birtaniya na tsawon zamani a tarihin Birtaniya.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.