Hamza Bin Laden: Amurka za ta ba da ladan ₦360m

State Department's Wanted poster Hakkin mallakar hoto Rewards for Justice/State department
Image caption Ba a san inda Hamza Bin Laden yake boye ba

Kasar Amurka za ta ba mutumin da ya ba ta bayanai game da daya daga cikin 'ya'yan marigayi Osama Bin Laden kyautar dala miliyan daya (kimamin naira miliyan 360 ke nan).

Hamza Bin Laden wanda ake nema ruwa a jallo shi ne shugaban wata kungiyar masu kaifin kishin Islama ta al-Qaeda, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Ana zaton yana rayuwa ne a kusa da iyakar kasar Afghanistan da Pakistan.

A 'yan shekarun nan, ya saki wani faifan murya da bidiyo inda yake kiran mabiyansa da su kai wa kasar Amurka da sauran kasashen yamma hari a wani martani ga kisan mahaifinsa.

A shekarar 2011, wasu dakaru musamman suka kashe Osama Bin Laden a wani gida dake garin Abbottabad a kasar Pakistan.

Marigayin ne ya kitsa kai harin ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001, inda akalla mutane kimanin 3,000 suka rasa ransu a Amurka.

A ranar Juma'a, ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta sanar da soke kasancewar Hamza Bin Laden zama dan kasarta.

A watan Maris din shekarar 2018, ya bayyana a wani faifan bidiyo, inda ya bukaci 'yan Saudiyya da su kaddamar da jahadi a kan masarautar kasar.

Labarai masu alaka