Mutum biyar sun mutu a hatsarin jirgin sama a Kenya

Helicopter Hakkin mallakar hoto Stephen Pond

Hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu ya rutsa da direban jirgin mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto da kuma Amurkawa hudu a wani tsibiri dake arewa maso yammacin Kenya kamar yadda 'yan sandan kasar suka bayyana.

Jirgin wanda Kaptin Mario Magonga yake tukawa kafin hatsarin, ya rikito a ranar Lahadi da misalin karfe 17:00 agogon GMT a wani tsibiri dake Central Island National Park dake tafkin Turkana, wani sanannan wurin yawon bude ido da hukumar kula da ilimi da al'adu ta majalisar duniya ta lissafa a matsayin wurare masu hatsari.

Har yanzu babu wani takamaiman dalili da aka bayyana a matsayin dalili na rikitowar jirgin, kuma ba a bayyana sunayen Amurkawan dake cikin jirigin ba.

Tuni dai aka tura jami'an tsaro wurin da hatsarin ya faru domin taimakawa wajen dauko gawarwakin da jirigin ya rutsa dasu.

Wannan hatsarin dai ya zo ne kwanaki biyar bayan wani jirgi ya yi hatsari a wani daji dake Kericho a kasar ta Kenya.

Labarai masu alaka