Kun san kasar da saba lokaci ba wani laifi ba ne?

A Ghanaian artist making a clock

Asalin hoton, AFP

Daga cikin jerin wasikun 'yan jarida daga Afrika, 'yar jarida a Ghana kuma tsohuwar minista Elizabeth Ohene ta bayyana dalilan da suka sa amfani da agogo ba shi da wani amfani a kasar Ghana.

Lokacin da aka tilasta wa ministar wasannin Olympics a Japan neman afuwar jama'a bayan ta yi lattin minti uku kafin shiga zauren majalisa, zan yi mamakin ministoci nawa ne a nan Ghana abin zai shafa, sun gode Allah ba a Japan suke ba.

Ba wani laifi ba ne a Ghana don wani mai rike da babban mukami ya yi lattin zuwa wani babban taro, domin an riga an saba dole sai sun yi latti.

Na san yadda wannan yake a halayenmu, saboda lokacin da ina minista idan na zo wurin taro cikin lokaci kamar yadda aka tsara, akan yi mamaki domin ba wanda ya yi tunanin zan iso da wuri.

Wasunmu da dama a gwamnati a lokacin mun yi tunanin idan har muka sa shugaban kasa isa taro cikin lokaci, zai iya sauya wannan al'adar.

Wadanda suka damu da shugaban kasa a lokacin John Kufuor suna da burin ganin ya dinga zuwa taro cikin lokaci.

Na tuna karon farko da ya isa taro a lokacin da aka tsara karfe 09:30 na safe, inda ya shammaci jami'an diflomasiya da manyan baki da Sarakuna suka rude suna ta hanzari su zauna kujerunsu, ba tare da tunanin shugaba Kufour zai iso da wuri ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Ghana na shammatar kansu kan lokaci inda suke cewa GMT na nufin "Ghana Maybe Time" wato lokacin Ghana da babu tabbas.

Mun ta yin kokarin ganin shugaban ya dore da zuwa taro cikin lokaci, da manufar cewa idan har mutane suka fahimci shugaba na zuwa taro da wuri, to kowa zai sauya.

Ana walakanta lokaci

Na kan ji takaicin yadda jami'an diflomasiyya da aka turo daga wasu kasashe suke bata lokacinsu suna jiran a fara taro, inda har ya kai sun saba kuma suka koma su kansu ba su isa taro cikin lokaci

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Nana Akufo-Addo a hagu da tsohon shugaba Kufuor sun yi kokarin mutunta lokaci

Bayan wani lokaci a Ghana, jami'an diflomasiyyar sun koma kamar 'yan kasa tare da amincewa babu wani taro da za a fara cikin lokaci.

Matsalolin na faruwa ne daga jami'an tsaro da kuma jami'an da ke hidima da jami'an gwamnati.

Suna dagewa kan cewa bai kamata shugaban kasa ya tafi wurin da ba a riga an kammala shiryawa ba.

A wajen rantsar da shi, shugaban kasa na yanzu Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya bayyana damuwa kan al'adar da ta zama ruwan dare ta saba lokacin soma babban taro.

Ya yi alkawalin zai zama abin misali domin zai dinga isa da wuri. Kuma tun daga lokacin ya yi kokarinsa na isa taro cikin lokaci.

Sai dai wannan bai zama dalilin kawo sauyi ga tabi'ar mutunta lokaci ba.

Cunkoson ababen hawa

Taron da aka shirya za a fara karfce 10:00, ba za a fara ba sai an yi karin sa'a daya.

Cunkoson ababen hawa da ake samu a manyan biranenmu wani lokaci shi ne dalilin da ya sa ake lattin zuwa taro.

Yana da wahala a iya kiyasta adadin lokacin da mutum zai isa, kuma da wannan ne wasu suke fakewa idan har sun yi latti isa taro.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana fara taro yawanci bayan awa daya da lokacin da aka tsara

Nisa tsakanin gidana zuwa Ofis da nake yawan zuwa zai dauke ni minti 20, ko 40 ko zuwa awa daya, wani lokaci na taba shafe awa daya da minti hamsin.

Sai dai cunkoson kuma ba zai taba zama dalili ba ga mutanen da aka gayyata cin wata liyafar abincin rana suka iso karfe 4:00 maimakon lokacin da aka gayyace su 12:30.

Ba zai taba yiyuwa ba ace mutum ya gayyace ka cin liyafar abincin rana kuma ya fara baka abincin misalin karfe 3:00, ko kuma ya gayyace ka cin abincin dare da misalin karfe 7:00 sai kuma ya fara baka abincin da misalin karfe 9:00 na dare.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yana da wahala a iya tantance lokacin kammala addu'o'i coci-cocin Ghana