Matan da ke amfani da Facebook don yaki da mayaudaran maza

Wasu mata a lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnatin Albashir Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu mata a lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnatin Albashir

Mata a kasar Sudan na amfani da wani zaure a shafin Facebook domin yaki da maza masu yaudara da masoyansu da kuma kin jinin gwamnati.

Shafin wanda aka kafa shekara uku da ta gabata ya zama wani jigo a kasar a yanzu.

"Minbar-Shat" wato "tsananin kauna" shi ne sunan shafin wanda ke da dubban masu amfani da shi a kasar.

Wani lokaci su kan saka hotuna da sunayen mazan da 'yan matan da suke tarayya da su domin jan kunnensu.

Duk da takunkumin da gwamnatin kasar ta sanya a kan shafukan sada zumunta da kuma takunkumi a kan amfani da intanet, matan na amfani da kungiyar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matan Sudan sun zama jigon kin jinin gwamnatin Albashir

Matan na yin amfani da wani boyayyen layi daga inda mutum yake amfani da intanet, watoVPN domin sada zumunta a wadannan shafukan.

Wasu matan sun shaida wa, Zeinab Mohammaed Saleh yadda jami'an shirri na kasar (NISS) suke cin zarafin wasu matan da aka kama a lokacin zanga-zanga.

Mata sun zama jigo a nuna kin jinin gwamnatin Al-Bashir inda wasu lokuttan su kan zama kashi 70 cikin 100 na masu halartar zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar.

Labarai masu alaka