Aisha Buhari ta ja kunnen jam'iyyar APC kan rabon mukamai

ais Hakkin mallakar hoto Aisha Buhari

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari ta shawarci jam'iyyar APC mai mulki da cewa idan an zo rabon mukamai to a yi hakan wajen bai wa mau katin jam'iyya kawai.

Hajiya Aisha ta bayar da wannan shawara ce a wajen wata liyafar cin abincin dare da aka gudanar a ranar Alhamis a Daura, don murnar nasarar da mai gidanta ya sake samu a karo na biyu.

A makon da ya gabata ne Shugaba Muhammadu ya kayar da babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, a zaben shugaban kasa da aka gudanar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Aisha Buhari ta fara bayar da shawara irin wannan ba ga mijinta ko jam'iyyarsa.

Hajiya Aisha ta ce kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC ya bayyana karara cewa masu katin jam'iyya kawai za a dinga bai wa mukamai, "a don haka ne ya kamata jam'iyya ta girmama kundintsarinta kamar yadda ya dace."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar BBC ta musamman da Aisha Buhari

Latsa alamar hoton da ke sama don sauraron hirar da Aisha ta taba yi da BBC inda ta soki gwamnatin mijinta.

A wajen taron dai uwargidan shugaban kasar ta kuma nuna godiyarta kan goyon bayan da jam'iyyar ta samu a lokacin zaben shugaban kasa, musamman ma daga mata da matasa inda ta tabbatar musu da cewa gwamnati za ta kara kaimi wajen inganta rayuwarsu.

"Ina so na godewa mata da matasan kasar nan kan yawan kuri'un da suka bai wa Shugaba Buhari a zaben 2019, kuma ina tabbatar musu da cewa zai ci gaba da bakin kokarinsa don mayar da Najeriya kasar da kowa zai ji dadinta," a cewar Aisha.


Makasudin Liyafar

Liyafar dai an shirya ta ne don murnar nasarar da mijinta ya sake samu a karo na biyu a matsayin shugaban Najeriya.

An yi liyafar ne a babban filin wasa na garin Daura, mahaifar Shugaba Buhari, kuma ya samu halartar mata da matasa magoya bayan APC daga daukacin jihar Katsina.

Daga cikin mahalarta taron har da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC kamar su ministan sufurin jiragen sama Sanata Hadi Sirika da shugabar mata da matasa ta APC ta yakin neman zaben shugaban kasa Binta Muazu, sa Sanator Fatuhu Mohammed mai wakiltar mazabar Daura.

Akwai kuma uwagidan gwamnan Katsina Zakiyya Masari da kuma matar ministan harkokin cikin gida Hadiza Dambazau.


Mace mai jawo ce-ce-ku-ce - Sharhi; Halima Umar Saleh

Hakkin mallakar hoto Aisha Buhari Twitter

Ana yi wa Hajiya Aisha Buhari kallon mace mai yawan jawo ce-ce-ku-ce kan al'amuran da suka shafi mulkin maigidanta.

A shekarar 2016 ne hakan ya fara fitowa fili bayan da ta yi wata hira da BBC Hausa inda ta ce wasu 'yan tsirarun mutane sun mamaye gwamnatin mijinta, Shugaba Muhammadu Buhari, suna hana ruwa gudu.

Ta yi zargin cewa ba a tafiya da wadanda suka sha wahalar kawo mijinta kujerar tasa wajen ba su mukamai, sai dai a dauko wasu can na nesa a ba su.

A wancan lokacin har ta yi ikirarin idan abubuwa ba su sauya ba to ba za ta mara masa baya a zaben 2019 ba.

Akwai kuma lokacin da ta soki jam'iyya mai mulki ta APC dangane da yadda ta gudanar da zabukan fitar da gwaninta a 2018.

Amma wasu da dama sun daganta hakan da rashin samun nasarar dan uwanta da ya tsaya takarar gwamnan Adamawa a APC din a zaben fitar da gwani.


Ga 'yan Najeriya da dama dai suna ganin abun da Aisha take yi bai dace ba, musamman ga tarbiyya irinta kabilar Hausawa da Fulani, amma a wani bangaren wasu kuma na ganin abun da Aisha ke yi daidai ne, domin gyara kayanka ne, wanda masu magana kan ce ba ya zama sauke mu raba.

Sai dai duk da sukar da take sha hakan bai hana ta yin gum da bakinta ba a duk lokacin da take zargin ana wani abu da bai dace ba a mulkin mijin nata.

Amma a baya-bayan ana ganin hotunan Aisha da mijinta na yaduwa a shafukan sada zumunta da muhawara da ke nuna yadda suke ji da juna, kuma ganin tun da aka fara yakin neman zabe har aka yi zabe ba ta yi korafi kan wani abu ba, ya sa wasu ke ganin kamar sun dinke barakar da ke tsakaninsu, (suna koren ganye).

Ko ma dai yaya abun yake, a yanzu a iya cewa 'yan Najeriya sun zuba ido don ganin yaya salon mulkin Buhari zai kaya a karo na biyu, kuma yaya matar tasa za ta kasance.

Shin za ta ci gaba da sukar duk wata manufa da ba ta yi mata ba ne, ko kuwa a wannan karon zuba ido za ta yi kan duk abun da ka iya faruwa.

Sai dai ga dukkan alamu wannan shawara da ta bai wa jam'iyyar APC a karon farko jim kadan bayansake lashe zaben mijin nata, yana nuna ba za ta ja da baya ba wajen daina tsoma baki a al'amarin da ya shafi mulkinsa ko jam'iyyarsa.


Wace ce Aisha Buhari?

An haifi Aisha Halilu ran 17 ga watan Fabrairun 1971 a jihar Adamawa da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Kakanta Alhaji Muhammadu Ribadu shi ne ministan tsaron Najeriya na farko.

Ta yi digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a fannin Public Admimistration, sai ta yi digirinta na biyu a kan harkokin kasashen waje.

Ta yi difloma a fannin kwalliya a makarantar koyon ado ta Carlton Institute da ke Windsor a Birtaniya, da kuma wata makarantar koyon gyaran jiki ta Academy Esthetique da ke Faransa.

Hakkin mallakar hoto NAna Buhari
Image caption Aisha Muhammadu Buhari da wasu daga cikin 'ya'yanta da na mijinta

Aisha Muhammadu Buhari da wasu daga cikin 'ya'yan Shugaba Muhammadu Buhari

Kafin maigidanta ya zama Shugaban Najeriya, tana da shagon gyaran jiki da kwalliya mai suna Hanzy Spa a jihar Kaduna.

Ta wallafa wani littafi na koyar da kwalliya da gyaran jiki wanda Hukumar da ke kula ta makarantun kimiyya da fasaha ta Najeriya ta sa shi a cikin manhajar da makarantun za su yi amfani da shi.

Aisha ta haifi 'ya'ya biyar da Muhammadu Buhari.


Karin Labaran da za ku so ku karanta