Dalilin da ya sa aka saki mataimakin gwamnan Kano, Gawuna

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kwamishinan 'yan sanda kan kama mataimakin gwamnan Kano

A ranar Litinin ne aka saki mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Gawuna bayan an kama shi ranar Lahadi da dare bisa zarginsa da yunkurin tafka magudin zabe.

An zargi Gawuna da shi da kwamishinan kananan hukumomin jihar da yayyaga sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa.

A yanzu dai an sake shi ne sakamakon kariya da yake da ita a matsayinsa na mataimakin gwamna.

Sai dai sauran mutanen da aka kamasu tare na nan tsare har yanzu a hannun 'yan sanda.

Yaushe aka kama mataimakin gwamnan jihar Kano?

'Yan sanda sun kama Gawuna mataimakin gwamnan Kano da kuma kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo ne a ranar 11 ga watan Maris.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun kama manyan jami'an gwamnatin jihar ne bayan da suka yi kokarin tayar da rikici a Nasarawa, karamar hukumar da ta rage a kammala tattara sakamakon zaben gwamna a Kano.

Wani hoton bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda aka cire wa kwamishina Garo kayan jikinsa, har sai da jami'an tsaro suka shiga tsakani.

Shin 'yan sanda na da hurumin kama shi?

Hakkin mallakar hoto NASIR
Image caption CP Muhammad Wakili

Wasu kwararru a fannin shari'a sun bayyana cewa hukumar 'yan sanda ba ta da hurumin kama mutum mai irin mukaminsa.

A cewar sashe na 308, sakin layi na daya da na biyu da na uku, jami'an tsaro ba su da hurumin kama shugaban kasa da mataimakinsa, ko gwamna da mataimakinsa.

Haka zalika ba su da hurumin da za su iya gurfanar da shi a gaban kotu ko kuma su gabatar da babba ko karamin laifi a kansa a gaban kowace irin kotu.

Amma wasu masu sharhi da wasu lauyoyin na ganin cewa rundunar 'yan sanda za ta iya kama shi a bisa "laruri" idan zai iya kawo lalacewar doka da oda a cikin al'umma.

Sai dai daga baya rundunar 'yan sandan ta ce ba kama mataimakin gwamnan ta yi ba "kubutar da shi ta yi," sai dai abun da ya daure wa mutane kai shi ne abun da kubutarwar ke nufi, bayan kuwa hukumar 'yan sanda aka kai shi a lokacin da suka tafi da shi din.


Ina bayyana sakamako ya kwana a Kano?

Hakkin mallakar hoto DOKAJI
Image caption An ci gaba da bayyana sakamakon

Kafin kama mataimakin gwamna Gawuna, an bayyana sakamakon kananan hukumomi 43 daga cikin 44 da ke akwai a Kano.

Wadda ta rage kawai Nasarawa ce wadda aka zargi 'yan APC da yaga sakamakon nata, a dalilin suna ganin tuni PDP ta sha gabansu a yawan kuri'u kuma suna fargabar abun da hakan zai jawo, kamar yadda masu sharhi suka bayyana.

Bayan aukuwar hakan, jami'an hukumar zabe ta kasa sun tattauna inda suka bayyana cewa za a ci gaba da hada sakamakon, sai dai ba su fadi takameme lokacin da za a yi hakan ba.

Image caption Manyan 'yan takarar kujerar gwamnan Kano

Zaman lafiya

Jigga-jigan manyan jam'iyyun guda biyu na Kano, Ganduje da Kwankwaso sun nemi jama'ar jihar da a zauna lafiya a bi doka.

Wannan na zuwa ne a ci gaba da zaman dar-dar da ake yi a cikin jihar inda ake jiran sakamakon zaben.

Tun ranar 9 ga watan na Maris wasu magoya bayan wasu 'yan takara suka fara murnar lashe zabe wanda hakan ya sanya rundunar 'yan sandan jihar ta yi gargadi da a daina a jira hukumjar zabe ta bayyana sakamako.

Hakkin mallakar hoto SADIQ_SB
Image caption Wasu masu murna a ranar 9 ga watan Maris