Kun san jihohin da INEC ta kammala zaben gwamna?

Twitter/@GovernorMasari Hakkin mallakar hoto Twitter/@GovernorMasari

A yanzu haka jihar Kano ta shiga jerin gwanon jihohin da INEC ta bayyana cewa ba a kammala zabe ba, jihohin da suka hada da Benue da Sokoto da Bauchi da kuma Plateau.

Hakazalika akwai zaben majalisar jihar Edo na mazabar Orhionmwon 2 da shi ma hukumar zbe INEC ta bayyana cewa bai kammala ba sakamakon matsaloli da aka samu, ciki kuwa har da satar kayan zabe.

Babbar jam'iyyar adawa a kasar ta bukaci magoya bayanta a fadin kasar da su matsa kaimi ga hukumar INEC ganin cewa biyar cikin shida na jihohin da aka bayyana zabensu a matsayin wanda bai kammala ba PDP ce a kan gaba.

Me yake jawo zabe ya zama wanda ba a kammala ba?

Image caption Jami'in zabe na jihar Kano Farfesa BB Shehu yana bayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammalu ba

Kamar yadda dokar zabe ta Najeriya ta samar, hukumar INEC za ta iya bayyana zabe a matsayin wanda bai kammala ba idan aka samu yawan kuri'un da aka soke sun zarce tazarar da ke tsakanin dan takarar da ya ci zabe da wanda ya zo na biyu a zaben.

Soke zabe a wasu rumfunan bai rasa nasaba ne da rashin tsaro da aka samu a wasu rumfunan da kuma wasu matsaloli a wasu wuraren da suka hada da zargin magudi.

Me zai faru bayan haka?

Image caption Magoya baya da 'yan jarida a kofar gidan Samuel Ortom bayan an bayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammala ba

Dokar Najeriya ta ce za a dauki kusan kwanaki bakwai bayan an sanar da sakamakon zabe kafin a fara shirye-shiryen sabon zabe a jihar.

Wannan zaben za a yi shi ne tsakanin wanda ya zo na farko da kuma kuma wanda ya zo na biyu a zaben da aka gudanar da bai kammala ba.

Amma jami'an zabe na jihohin shida sun bayyana cewa za a je zagaye na biyu na zaben nan da mako uku.

Zaben zai gudana a rumfunan zaben da aka soke ne kawai.

Su wa suka lashe zaben gwamnoni da ya kamalla?

Image caption Wata kenan da ke murnar Abdullahi Sule ya lashe zaben gwamna a jihar Nasarawa

A yanzu haka hukumar INEC ta bayyana sakamakon zaben da aka yi a wasu daga cikin jihohi 29 da aka gudanar da zabuka a kasar.

Jerin jihohin da INEC ta bayyana zabensu a matsayin wanda aka kammala:

 • Abia - Okezie Ikpeazu (PDP)
 • Akwa Ibom - Udom Emmanuel (PDP)
 • Borno - Babagana Umara Zulum (APC)
 • Cross River - Ben Ayade (PDP)
 • Delta - Govnor Ifeanyi Okowa (PDP)
 • Ebonyi - David Umahi (PDP)
 • Enugu - Ifeanyị Ugwuanyi (PDP)
 • Gombe - Alhaji Inuwa Yahaya (APC)
 • Imo - Emeka Ihedioha (PDP)
 • Jigawa - Mohammadu Badaru Abubakar (APC)
 • Kaduna - Govnor Nasir El-Rufai (APC)
 • Katsina - Aminu Masari (APC)
 • Kebbi - Abubakar Atiku Bagudu (APC)
 • Kwara - Abdulrahman Abdulrazaq (APC)
 • Lagos - Babajide Olusola Sanwo-Olu (APC)
 • Nasarawa - Abdullahi Sule (APC)
 • Niger - Govnor Abubakar Bello (APC)
 • Ogun - Prince Dapo Abiodun (APC)
 • Oyo - Seyi Makinde (PDP)
 • Taraba - Darius Ishaku (PDP)
 • Yobe - Alhaji Mai Mala Buni (APC)
 • Zamfara - Muktar Idris (APC)