Kawunan masana shari'a ya rabu kan zaben Kano

Manyan 'yan takarar kujerar gwamna a Kano
Bayanan hoto,

Hukumar INEC ta ce za a sake zabukan ne wasu mazuka a ranar 23 ga watan Maris

Jihar Kano ta shiga jerin gwanon jihohin da INEC ta bayyana cewa ba a kammala zaben ta ba, jihohin da suka hada da Adamawa da Benue da Sokoto da Bauchi da kuma Plateau.

Barister Bulama Bukarti da Barrister Mai Nasara Kogo Umar sun bayyana mabambantan ra'ayoyi game da batun rashin bayyana wadanda suka lashe zabe a wadannan jihohi.

Bukarti ya ce bai kamata a soke zaben wadannan jihohin ba, yayin da Barrister Kogo yake ganin akwai hujjoji masu karfi da suka sa hukumar INEC ta ki bayyana sakamakon zabukan.

Bukarti a nasa ra'ayin yana ganin cewa akwai yiyuwar kotu ta saurari jam'iyyar da ke korafi game da matakin, wata kila ma kotu ta tabbatar musu da nasararsu. ba tare da an sake zabe ba.

 • Latsa alamar lasikika a kasa domin sauraron yadda muhawarar ta kasance.

Kun san jihohin da INEC ta kammala zaben gwamna?

Jerin jihohin da INEC ta bayyana zabensu a matsayin wanda aka kammala:

 • Abia - Okezie Ikpeazu (PDP)
 • Akwa Ibom - Udom Emmanuel (PDP)
 • Borno - Babagana Umara Zulum (APC)
 • Cross River - Ben Ayade (PDP)
 • Delta - Govnor Ifeanyi Okowa (PDP)
 • Ebonyi - David Umahi (PDP)
 • Enugu - Ifeanyị Ugwuanyi (PDP)
 • Gombe - Alhaji Inuwa Yahaya (APC)
 • Imo - Emeka Ihedioha (PDP)
 • Jigawa - Mohammadu Badaru Abubakar (APC)
 • Kaduna - Govnor Nasir El-Rufai (APC)
 • Katsina - Aminu Masari (APC)
 • Kebbi - Abubakar Atiku Bagudu (APC)
 • Kwara - Abdulrahman Abdulrazaq (APC)
 • Lagos - Babajide Olusola Sanwo-Olu (APC)
 • Nasarawa - Abdullahi Sule (APC)
 • Niger - Govnor Abubakar Bello (APC)
 • Ogun - Prince Dapo Abiodun (APC)
 • Oyo - Seyi Makinde (PDP)
 • Taraba - Darius Ishaku (PDP)
 • Yobe - Alhaji Mai Mala Buni (APC)
 • Zamfara - Muktar Idris (APC)