Zakarun Turai: Juventus ta fitar da Atletico Madrid 3-0

Karo na takwas da Cristiano Ronaldo ya ci kwallo uku rigis a gasar Zakarun Turai Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cristiano Ronaldo lokacin da ya ci bal dinsa ta 122 a gasar ta Zakarun Turai, kafin kuma ya kara biyu bayan hutun rabin lokaci

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo uku rigis wanda hakan ya sa Juventus ta yi waje da Atletico Madrid, ta kuma kai wasan dab da na kusa da karshe na gasar Zakarun Turai.

A wasansu na farko a Madrid Atletico ce ta ci Juventus 2-0, amma reshe ya juye da mujiya a wannan karawa ta Italiya, Juventus ta rama biyun har ma ta kara dayar da ta ba ta nasarar zuwa matakin na gaba da ci 3-2 gida da waje.

Cristiano Ronaldo ya ci kwallon farko ana minti 27 da wasa, sannan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci da minti hudu kacal ya kara ta biyu duka da ka.

Ana saura minti hudu lokaci ya cika na ka'idar minti 90 sai Juventus ta samu fanareti bayan da Angel Correa ya yi wa Federico Bernardeschi keta, sai dan wasan na Portugal ya buga fanaretin ya ci.

Bal din da ya ci ta ukun ta kasance ta 124 kuma karo na takwas da ya ci uku rigis a gasar Zakarun Turai.

Tashi daga wasan ke da wuya sai magoya bayan kungiyar ta Italiya suka barke da sowa, su kuwa 'yan wasan na Juventus suka yi kan Ronaldon mai shekara 34 cike da murna.

Hakkin mallakar hoto Semi Khedira
Image caption Dan wasan Juventus na tsakiya Semi Khedira ya sanya wannan hoton na 'yan wasan bayan sun yi nasara

Rashin nasarar ya sa Atletico ta rasa damar yin wasan karshe na gasar ta Zakarun Turai ta bana a filinta na Wanda Metropolitano ranar 1 ga watan Yuni.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hari daya kawai Antoine Griezmann ya kai a wasan

A ranar Juma'a ne za a fitar da jadawalin wasan matakin na dab da na kusa da karshe, na kungiyoyi takwas da karfe 11 na safe agogon GMT.