Yadda za ku daina jin tsoron hawa jirgi

Worried woman on plane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu mutane, zama a cikin jirgi kan haddasa musu bacin rai mai yawa

Bayan hadarin jirgin da ya faru a kwanan nan mutane da dama na jin tsoron yin tafiya ta jirgin sama, sai dai kuma kididdigar hadarin zirga-zirgar jiragen ya yi sauki, inda a kan samu hadari daya daga jirage miliyan 2.5 da suka tashi a bara.

Shin yaya za ku shawo tsoron tafiye-tafiye da shiga jirgin sama? Ga wasu shawarwari da masana ilimin kwakwalwa suka bayar.

Shin tafin hannunka yana yin gumi idan ka shiga jirgin sama? Kana kama hannun kujera gam idan jirgi zai tashi sama? Kana jin zuciyarka tana bugawa da sauri a lokacin da jirgin sama zai sauka?

Kamar kai - kaso 17 cikin 100 'yan Amurka (kamar yadda wani bincike Kididdigar da Boeing ya fitar suna jin tsoron tafiya a jirgin sama.

Bayan da jirgin sama na Ethiopia samfurin 737 ya yi hadari har da yin sanadin mutuwar mutum 157 - kowa ya san cewar abun fargaba ne. Amma a kan dade kan jirgin sama ya yi hadari.

A kididdigar da aka bayar ta zirga-zirgar jiragen sama a duniya ya kai tashin jirgi miliyan 37,800,000, inda hadari daya kan faru a tashin jirgi miliyan 2,520,000 in ji Kididdigar hadarin jirgin sama a 2018 kididdiga da hukumar kare hadarin jiragen sama (ASN) ta fitar.

Sai dai kuma saboda ana yada hadarin jirgi, shi ya sa tsoronmu kan karu.

Abin farin ciki za a iya magance fargabar hawa jirgi - hala ma akwai hanyoyin da za a bi don magance hakan. Ga shawarwarin da likitocin kwakwalwa suka bayar.

Atisayen shakar iska

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masalin ilimin kwakwalwa Matthew Price ya ce jan dogon numfashi a jirgi kan rage fargaba

Da akwai mutane da suke jin tsoron tafiya a jirgin sama saboda ba su taba hawa ba ko ba su taba cin karo da wani abu na tashin hankali ba a lokacin da suke balaguro, masanin kwakwalwa a jami'ar Vermont, Matthew Price ya yi bayani.

''Abin takaici, babu wata hanya da za a yi bayanin dadilin da mutane suke jin tsoro, amma da akwai dalilai da dama da sukan sa ake jin tsoron''.

Ya kara da cewa ''Zai iya faruwa tashin jirgin ne a zahiri, ko sanin hadarin jirgin sama, ko jin yadda mutum ke sararin samaniya.''

Prince ya bayar da shawarar yin atisayen shakar iska - za ka tsaya na dan lokaci ka ja iska ta bakinka sai ka fitar da ita ta hancinka - sai ka ci gaba da yin haka ka kuma kwantar da hankalinka.

Abinda ya kamata ka yi

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tattauna wa kan tashin hanakalin da ka shiga kan sa mutum ya samu sauki

Wasu kan rufe kunnensu don su dauke hankalinmu a lokacin da suke jirgin sama, wasu kan sha maganin bacci - wasu kan sha barasa.

Sai dai idan tsoron gabaki daya kan hana sukuni - har ma ya hana ka shiga jirgin sama, da akwai hanyoyi da dama da ya kamata a bi.

A kan duba dabi'a ko halayyar kwakwalwa ko shawarwari da za a bayar - duk zai taimaka don magance jin tsoro a lokacin tafiya a jirgin sama.

Hakan na nufin sanin hanyoyin sigar tashin hankali, fayyace yadda abin kan fara da kan kai mu ga jin tsoro da - abu mafi mahimmaci - yadda za ka magance abin da kake ji.

Fuskanci abin da ke baka tsoro

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Saka kanka a yanayi na kana cikin jirgi da ake amfani da shi a yanzu haka kan taimaka wajen fargabar jirgi.

Masana sun ce hanyar da ta fi dacewa ka shawo kan fargaba a lokacin tafiya a jirgin sama ''ka yi kokarin shawo kan fargaba''.

Kamar yadda masu magana kan ce ''fuskanci abin da ke baka tsoro'', idan a hankali muka nuna kanmu ta hanyoyi da dama a lokacin tashin jirgi, a kulawa ta kwararren likita ko kuma masanin kwakwalwa.

Da akwai bita ta musamman da ta maida hankali kan ''tafiya a jirgin sama ba tare da fargaba ba'' wani shiri ne da Virgin Atlantic kan gudanar.

Ya hada da amsa tambayoyi daga matuka jirgin sama, inda suke fayyace abubuwa da suka shafi tsoron tafiya a jirgi da yadda jirgin ke tafiya, me ya sa jijjigar jirgin sama ba komai ba ce, menene kamfanin jirage ke yi kan kunar bakin wake da abubuwa kamar me matuka jirgin sama ke yi idan inji ya samu matsala.

Wata kwararriyar likitar kwakwalwa Barbara Rothbaum ta jami'ar Emory ta Atlanta a Georgio, ta kwatanta magance bayyana fargaba da rashin tsoro da zahirin tafiya a cikin jirgin sama.

''Kaso 93 cikin 100 da aka gwada a shirin, sun shiga jirgi bayan duba su da aka yi, kuma bita takwas da aka yi musu ta magance fargabar,'' ta kuma ce zangon farko daga hudu sun nuna wa mutane yadda ake magance fargaba, ta kara da cewar misali, yadda za ka fayyace tunani mara kangado ko na babu gaira babu dalili ( misali '' za mu yi hadari,'') sai ka gyara tunanin.

Sauran zango hudu sun yi amfani da kusan zama gaskiya domin taimakawa mutane su yaki fargaba ta yadda tsoron da suke ji zai yi kasa matuka.

''Hakan na nuna hanya ta yin aiki zahiri da jirgin sama na ainihi ko kuma kwatanta jirgin, ta yadda damar da za ka fahimce abin da ake nufi za ta fito maka karara - kuma ta kudi kankani ta yadda za ka tuka jirgi ka kuma sauka iya yawan da kake so duk a minti 45 ta hanyar dabarun neman lafiya ba tare da mutum ya bar ofis ba'' in ji Rothbaum.

Fatan shi ne samar da ilimin neman lafiya, fahimta da kuma yadda za a magance abubuwa. Manufar shi ne idan ka fahimci abu, ba zai mamaye ka ba.

Kalli hanyoyin da za ka magance fargaba

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shekarar 2017 ita ce mafi karancin hadari a tarihin zirga-zirgar jirgin fasinjoji

Idan jirgi ya yi hadari labari ne mai girma. Musamman wanda ya auku a ranar 10 ga watan Maris, 2019 a lokacin da Ethiopian Airlines Boeing 737 Max ya fadi kasa minti shida da tashi daga filin sauka da tashin jirgin sama ma Addis Ababa.

Dukkan wadan da ke cikin jirgin su 157 suka mutu.

Sai dai masana sun ce an fi mutuwa a hadarin mota fiye da a jirgin sama, kuma hadarin jirgin sama ya raguwa a shekara 20.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce an yi hadarin mota da aka mutu a duniya sau miliyan 1.25 a shekarar 2013.

Jumulla hadarin mota ya fi tsamari sau 100 fiye da na jirgin sama, haka zalika abu biye ne ke kashe mutum farar daya shi ne bugun juciya da cutar daji.

Shekarar 2017 ita ce wadda aka samu mafi karancin hadarin jirgin sama in ji wani bincike da aka yi.

Babu wani jirgin fasinjoji da ya fadi a duniya, wani rahoto na daban da wasu masana a Dutch To70 da ta hanyoyin kiyaye hadari ta The Aviation Safety Network.

A shekarar 2018 hadari daya kacal aka samu a cikin zirga-zirga jirage miliyan 2.5 in ji babban jami'in Aviation Safety Network, Harro Ranter wan da ya kara da cewar an samu karin hanyoyin kiyaye hadararruka.

''Hakan ya nuna gagarumin ci gaba da aka samu a hanyar kiyaye hadarurruka a shekara 20,'' kamar yadda ya fada.

Mun zakulo muku labarin daga BBC FUTURE

Labarai masu alaka