Mutum 11 ne suka mutu a rushewar gini a Legas

rushewar makaranta a Legas
Image caption Ana ci gaba da aikin ceton a wurin da abin ya faru

Masu aikin ba da agaji a Legas na ci gaba da ceto mutanen da ke karkashin baraguzan ginin da ya rushe a ranar Laraba a unguwar Ita-Faaji da ke yankin Island a birnin.

'Yan sanda sun shaida wa BBC zuwa yanzu mutum 50 aka zakulo yayin da mutum 11 kuma suka mutu.

Gwamnatin Jihar Legas ta ce za a gudanar bincike bayan an kammala aikin ceto, kuma za a hukunta duk wanda aka kama da laifi.

Zai yi wahala a san takamaiman yawan mutanen da ke cikin ginin a lokacin da abun ya faru, saboda gini ne mai dauke da gidajen mutane da kuma makarantar da ke da dalibai kusan 100.

Makarantar na hawa na uku, sannan gidajen mutane ne a hawa na tsakiya sai kuma shaguna da ke kasa.

Mazauna yankin sun ce baya ga ginin da ya rushe din, akwai wasu gidajen da aka yi musu alamar cewa a rusa su amma sai masu su suka goge fentin alamar da gwamnati ta saka.

A Najeriya dai amfani da kayan gini marasa inganci ya zama ruwan dare.

A hannu guda kuma, 'yan uwa da dangin wadanda abun ya shafa suna ta tururuwar zuwa asibitoci ukun da aka kai mutanen don duba su.

Wasu sun ji sanyi a rayukansu ganin 'yan uwansu na nan da ra, amma an ga da dama na kuka don rashin ganin 'yan uwansu da 'ya'yansu da ke makarantar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Makaranta ta rushe ta kashe dalibai da dama a Legas

Shugaban kasa ya jajanta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar ruftawar wani bene a jihar Legas.

Ana fargabar cewa dalibai da dama sun mutu, yayin da ginin wata makaranta ya rufto a kansu a birnin Legas da ke Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba.

Har ila yau, shugaban ya bukaci gwamnatin jihar da dauki matakan da suka dace wajen kiyaye faruwar hakan a nan gaba.

Ganau

Wasu ganau mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa sau biyu gwamnati ke bai wa masu ginin umarnin cewa ka da a kara dora wani bene a kai, "amma sai suka yi biris da wannan umarni," in ji wani mutum.

Makarantar dai tana hawa na uku ne na ginin. Hotunan da aka dauka bayan ruftawar ginin sun nuna tarkace da baraguzai.

Wakilin BBC Hausa a Legas Umar Elleman ya ce an shafe yinin ranar Laraba ana ta faman aikin ceto don fiddo mutane daga baraguzan.

Za ku iya ganin wajen da abun ya faru a shafin BBC Yoruba na Facebook don kallon yadda kae aikin ceto Kai-Tsaye daga wurin...

Me hukumomi ke cewa?

Mai magana da yawun hukumar bayar da agaji ta gaggawa Ibrahim Farinloye,yace al'amarin ya faru ne da misalin karfe 10.30 na safe.

"An yi amannar cewa mutane da dama da suka hada da yara sun makale karkashin baraguzan ginin," a cewarsa.

Umar Elleman ya ce: "Wasu daga cikin wadanda aka fiddo zuwa yanzu sun fita a hayyacinsu, amma mazauna unguwar sun ce akwai mutuwa. Ni dai na shaida ceton yara uku."

Yawan rushewar gini a Najeriya

Ana yawan samun rushewar gine-gine a Najeriya musamman a manyan biranen kasar Legas da Abuj da Fatakwal, abun da ke jawo asarar rayuka da dumbin dukiya.

A shekarar 2014 kawai kusan sama da mutum 120 ne suka mutu sakamakon wannan iftila'in a Legas.

A watan Disambar shekarar 2016 ma wani ginin coci ya rushe a Legas din inda akalla mutum 116 suka rasa rayukansu.

Hakazalika a watan Maris din shekarar 2016, wani gini da ba a kammala gininsa ba ya rufta a gundumar Leki, inda mutum 34 suka mutu, aka ceto wasu 13 da ransu daga buraguzai.

An shafe kwana biyu ana aikin ceto a wancan lokacin.

A 2016 din dai kuma fiye da mutum 100 ne suka mutu bayan da wani ginin coci ya rufta a kansu a birnin Uyo da ke kudancin Najeriya.


Matsalar rushewar gine-gine a Najeriya

Yawan rushewar gine-gine da ake samu a Najeriya cikin shekaru ashirin da suka gabata abun damuwa ne matuka, saboda yadda ake samun asarar rayuka da dukiya sakamakon hakan.

Masana sun bayyana abubuwa da dama a matsayin wadanda ke jawo rushewar gine-ginen da suka hada da aikace-aikacen dan adam da ko kuma wata kaddara daga Ubangiji.

Hakan yana da matukar illa ga al'umma da kuma zuba jari a bangaren gine-gine.

Abubuwan da ke jawo rushewar gini

 • Kayan gini marasa inganci
 • Rashin aiki mai kyau
 • Rashin saka tubali mai kyau
 • Rashin amfani da kwararru a harkar gini
 • Cin hanci da ya dabaibaye bangaren gine-gine
 • Rashin bin ka'idojin da dokokin gine-gine
 • Rashin kula
 • Rashin bin shawarar kwararu
 • Rashin tsara gini yadda ya kamata
 • Dora kaya fiye da kima
 • Mamakon ruwan sama
 • Saba ka'idojin gini na hukuma.

Labarai masu alaka