Hotunan yadda ginin makaranta ya kashe dalibai a Legas

Image caption Al'amarin ya faru ne unguwar a Itafaji da ke yankin Legas Island.
Image caption Ginin dai mai hawa uku ne kuma akwai mutane da dama a cikinsa a lokacin da abin ya faru.
Image caption Tuni jami'an agajin gaggawa da 'yan kwana-kwana da masu aikin ceto na sa kai suka yi ta kokarin ciro da wadanda abun ya rutsa da su a karkashin baraguzan ginin.
Image caption Tuni dai aka garzaya da wasu daliban babban asibitin gwamnati da ke Marina, yayin da iyaye kuma ke turuwar zuwa wajen don duba 'ya'yansu.
Image caption Wasu ganau mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa sau biyu gwamnati ke bai wa masu ginin umarnin cewa ka da a kara dora wani bene a kai, "amma sai suka yi biris da wannan umarni," in ji wani mutum.
Image caption Ana yawan samun rushewar gine-gine a Najeriya musamman a manyan biranen kasar kamar Legas da Fatakwal da Abuja.
Image caption Wannan al'amari dai ya jefa mazauna yankin cikin matukar rudani da kaduwa.

Labarai masu alaka