Kotu ta ki sauraren karar rikicin APC a Zamfara

Sanata Kabiru Marafa Hakkin mallakar hoto ORDER PAPER
Image caption Sanata Kabir Marafa

Kotun daukaka kara ta dage sauraren shari'ar rikicin APC a Zamfara bayan bangaren da ya shigar da karar ya ce bai yadda da alkalan kotun ba.

Bangaren Sanata Marafa ne ya daukaka kara a Sokoto domin kalubalantar hukuncin da kotun tarayya a Gusau ta zartar cewa an yi zaben fitar da 'yan takara na jam'iyyar APC a Zamfara.

Barista Misbahu Salahundin daya daga cikin lauyoyin da ke kare Senta Marafa ya shaida wa BBC cewa Alkalan kotun daukaka karar ne suka ki sauraren karar.

"Bayan mun hallara a gaban kotu sai magatakarda ya fito ya ce manyan alkalai da aka turo sun ce ba za su zauna ba," in ji shi.

Karar da aka dage dai na zuwa ne bayan kammala zaben gwamna a Zamfara inda hukumar zabe ta sanar da Muktar Shehu Idris dan takarar bangaren gwamnati a jam'iyyar APC da ake kalubalanta a matsayin wanda ya lashe zaben.

Wata Kotun daukaka kara a Abuja ce ta bai wa hukumar zabe INEC umurnin ta amince da 'yan takarar APC a Zamfara, bayan da a farko INEC ta ki amincewa da 'yan takarar jam'iyyar saboda ta gaza yin zaben fitar da 'yan takara.

Lauyan gwamnati Barista Suraj Gusau ya ce yanzu suna jiran lokacin da za a sake sauraren karar bayan sun halarci zaman kotun daukaka karar a Sokoto da ba a zauna ba a ranar Laraba.

Bangaren Marafa ya rubuta takarda zuwa ga Alkalin alkalan kotun daukaka kara mai shari'a Zainab Balkachuwa inda suka nemi a a sake alkalan da za su yi shari'ar saboda ba su yadda da wadanda za su saurari karar da suka daukaka ba.

"Yanzu muna jiran sabbin alkalan da za a turo domin sauraren shari'ar," in ji Lauyan Sanata Marafa, Barista Misbahu.

Wa'adin daukaka karar dai wata biyu ne, kuma yanzu saura kwana 12 ya rage wa'adin karar da Marafa ya daukaka ya cika. Hakan na nufin shari'ar ba za ta wuce kwana 12 ba kenan.

Asalin rikicin APC a Zamfara

Hakkin mallakar hoto @Koguna
Image caption Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari mai barin gado tare da Muktar Shehu Idris da aka zaba a APC

Rikicin na APC a Zamfara ya samo asali ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha'awar takarar gwamnan a jam'iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da Sanata Marafa da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.

Sau biyu ana shirya zaben fitar da gwanin a jihar, amma sai a soke shi saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam'iyyar a jihar.

Dan takarar bangaren gwamnan jihar ne yanzu hukumar INEC ta amince da shi bisa umurnin Kotu wanda kuma ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 9 ga Maris.

Bangaren gwamnatin ya yi nasara ne a kotun daukaka kara a Abuja wacce ta soke hukuncin wata babbar kotun tarayya a Abuja, ya tabbatar da matsayin hukumar zaben kasar na haramta wa duk 'yan takarar jam'iyyar APC daga Zamfara shiga zabukan kasar.

Yanzu kuma daya bangaren na APC a Zamfara na kalubalantar hukuncin da Kotun Gusau ta zartar cewa an yi zaben fitar da 'yan takara a Zamfara.

Labarai masu alaka