Zaben 2019: ‘Yan Gandujiyya da Kwankwasiyya sun yi taron addu’o’i a Kano

Magoya bayan Gwamna Abdullahi Ganduje na APC da na Abba Kabir Yusuf sun gudanar taron addu'o'in neman nasarar kowannensu a zabukan da za a sake a wasu mazabu a jihar.

Bayanan hoto,

Magoya bayan Gwamna Ganduje sun gudanar da taron addu'o'in ne a karamar hukumar Dala

Bayanan hoto,

Tun bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da cewa zaben jihar bai kammala ba, ake samun fargaba a jihar

Bayanan hoto,

Jiga-jigan manyan jam'iyyun jihar Kano, Ganduje da Kwankwaso sun nemi jama'ar jihar da su zauna lafiya

Bayanan hoto,

Abba Kabir Yusuf ya samu kuri'a 1,014,474, yayin da Gwamna Ganduje ya samu kuri'a 987,819 bayan kidaya kuri'un da aka kada a zaben ranar Asabar

Bayanan hoto,

Kazalika, magoya bayan Kwankwasiyya su ma sun gudanar da tarukan addu'o'i a filin gidan Sarkin Kano

Bayanan hoto,

Sai dai fadar sarkin Kano ta ce ba a nemi izininta ba kafin fara taron addu'o'in

Bayanan hoto,

Kuma daga bisani an kori masu taron addu'o'in daga filin gidan sarkin

Bayanan hoto,

A ranar Asabar 23 ga watan Maris za a sake gudanar da zabe a wasu mazabu da a jihar