An kama masu sayen katin zabe a Nassarawa ta Kano

Kudi

Rudunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da kama wasu mutane biyar da take zargi da sayen katin zabe a unguwar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa a jahar kano da ke arewacin kasar.

Kakakin rundunar a jihar DSP Abdullahi Haruna Kyawa, shi ne ya tabbatar wa da BBC hakan, inda ya ce an kama mutanen ne bayan da suka samu labari.

Mutanen dai sun hadar da maza da mata, kuma ba a karamar hukumar Nassarawar kadai aka samu irin wadannan mutanen ba, har da karamar hukumar Dala inji jami'in.

Ya ce, da kyar suka kwaci mutanen daga hannun mutanen unguwannin da suka je sayen katin zaben.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce, dama tuni sun fuskanci cewa akwai wasu laifuka da mutane kan aikata a lokuta kamar kafin zabe da laifukan lokacin zabe da kuma na kafin a karasa zabe wato irin yanayin da Kanon ke ciki ke nan.

Jami'in dan sandan ya ce ya kamata mutane su sani cewa ' Hukumar 'yan sanda na sanar da su cewa saye da sayar da katin zabe babban laifi ne'.

Ya ce laifin ba wai na masu sayen katin zaben ba ne kadai, har ma su kansu masu sayarwan suma ya shafe su.

DSP Abdullahi Haruna Kyawa, ya ce ' Zamu bi lungu da sako mu kamo duk wanda ya aikata irin wannan dabi'a, da wanda ya saya da ma wanda ya sayar dukkansu masu laifi ne, kuma za a yi bincike a kansu sannan a gurfanar da su a gaban shari'a'.

Jihar Kano dai ta shiga jerin gwanon jihohin da INEC ta bayyana cewa ba a kammala zaben ta ba, jihohin da suka hada da Adamawa da Benue da Sokoto da Bauchi da kuma Plateau.

Hukumar ta INEC ta sanar da cewa za a sake gudanar da zabukan a ranar 23 ga watan Maris, 2019 a jihohin da ta sanar da cewa ba a kammala zabensu ba.

Sayen kuir'a a zaben gwamnoni

Wani al'amari da ya bai wa mutane da dama mamaki a yayin da ake zaben gwamnoni a jihohi 29 na fadin Najeriya, shi ne batun yadda ake sayen kuri'un mutane da kudi ko kayan masarufi ya zama ruwan dare gama duniya.

Wannan abu dai ya fara yawaita ne tun a ranar Juma'a wato jajiberin zaben. Sannan kuma wakilan BBC daga sassa daban-daban na Najeriya sun tabbatar da hakan, don kuwa su ganau ne ba jiyau ba.

Sayen kuri'un mutane dai a lokacin zabe babban laifi ne a dokar hukumomin kasar da ke yaki da cin hanci da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati.

A ranar Juma'a wakilan BBC da ke Jihohin Kwara da Legas sun ga yadda wasu jam'iyyu suke rabon kananzir da taliya da shinkafa ga mutane.

Haka zalika a ranar Asabar da ake gudanar da zaben, an ga yadda jam'iyyu ke rabawa mutane naira 200 ko 100 a wasu yankunan don su zabe su.

A ina aka yi rabon kudin?

Alal misali, a kusan daukacin jihohin kasar an samu rahotannin sayen kuri'un mutane.

Wata baiwar Allah da ta bukaci a sakaya sunanta daga Katsina, ta ce "Wallahi a kan idona na ga jam'iyyu biyu suna sayen kuri'un mutane. Daya jam'iyyar tana saya a kan naira 250 dayar kuma a kan naira 200.

"Ko ni sai da wakiliyar wata jam'iyya ta so latsa ni, amma ta ga ba fuska sai ta kyale ni," in ji ta.

A Legas ma an samu rahotannin sayen kuri'a da kudi ko wani abun amfani.

EFCC ma ta yi kamu

Hukumar EFCC ma ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta kama wasu makudan kudade da take zargin za a yi sayen kuri'u ne da su a jihar Benue.

A kokarinta na kama wadanda ke dauke da kudin ne ma, wasu 'yan daba suka kai wa jami'an hukumar hari tare da lalata motar bas din da EFCC din ke sintiri da ita.

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

A ranar Juma'a da daddare ma, jami'an tsaro sun kama wata mota kirar Jif shake da kudi, wanda suka yi zargin cewa za a yi sayen kuri'u ne da su.

Kazalika wasu rahotanni sun ce EFCC ta kama babban akawun jihar Imo Uzoho Casmir, bisa zarginsa da taimakawa Gwamna Rochas Okorocha da halatta kudin haram har dala biliyan 1.05 a zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki a ranar Asabar.

Hukumar dai tun a ranar Alhamis zuwa Juma'a ta tsaya kai da fata a filayen jiragen sama inda ake kai kayan zabe, don tabbatar da cewa babu makudan kudin da za a iya sayen kuri'u da su.

Me doka ta ce kan sayen kuri'a?

Hukumomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati na EFCC da ta yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC sun bayyana sayen kuri'a a matsayin laifin cin hanci.

Ko a wani taron wayar da kai da ICPC ta gudanar a watan Disambar 2018 ta ce sayen kuri'a zamba ce a dimokradiyya.

A wancan lokacin shugaban hukumar ya shawarci 'yan Najeriya da su guji biyewa marasa kishin kasa masu yaudararsu da kudi ko abun masarufi.

"Idan har ku ka bar su suka yi nasara ta hanyar yin hakan, to kuwa za su tabbatar sun sace dukiyarku da aka ware don samar da ruwan sha da inganta harkar lafiya da ilimi da gina tituna idan har suka hau," a cewarsa.