INEC ta mika takardar shaida ga 'yan takarar da suka yi nasara
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

INEC ta ba 'yan majalisar tarayya shaidar cin zabe

Hukumar zabe ta kasa INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga zababbun gwamnoni da 'yan majalisar tarayya na kasar a ranar Alhamis.

An gudanar da bikin ne a dakin taro na International Conference Center da ke a Abuja.

Hukumar ta ba sanatoci 104 takardar shaidar, sai kuma 'yan majalisar wakilai 346.