Yadda wasan Dara ya yi sanadin daukakar wasu yaran Legas
Yadda wasan Dara ya yi sanadin daukakar wasu yaran Legas
Wasu yara a unguwar marasa galihu a jihar Legas, wasan Dara ya yi masu sanadin samun tallafin karatu da daukaka a rayuwarsu.
Yaran sun samu tallafi saboda kwarewar da suka yi a wasan wanda ke gayatar da jama'a.
Yaran sun bayyana cewa wasan Dara ya yi tasiri a rayuwarsu saboda yana taimaka masu wajen fahimtar lissafi da tunani mai kyau.