Gini ya rufta da mutane a Ibadan

Rushewar gini

Ana ci gaba da aikin ceto jama'a a wajen da wani bene mai hawa uku ya rushe a Ibadan babban birnin jihar Oyo a Najeriya.

Lamarin ya faru ne kusan kwana hudu bayan wani gidan mai hawa uku shi ma ya ruguje a jihar Lagos, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 20.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe shida saura minti 15 na yamma a ranar Juma'a a unguwar Sogoye da ke Molete a Ibadan din.

Zuwa yanzu dai ba a iya sanin yawan mutanen da hadarin ya rutsa da su ba.

Rahotanni na nuna cewa an samu jinkirin gudanar da aikin ceton sakamakon rashin kayan aiki.

Amma da farko an ruwaito kakakin gwamnatin jihar ta Oyo, Mista Mr. Toye Arulogun, na cewa suna tafiyar da komai yadda ya kamata, babu wata damuwa.

Gidan mai hawa uku wanda ake kan aikin gininsa ya rufta ne kwatsam, ya jikkata mutane da dama wasu kuma buraguzai suka binne su.

Labarai masu alaka