Christchurch: An fara shari'ar mutumin da ya kashe Musulmi a New Zealand

Brenton Tarrant, mai shekara 28 a kotu
Bayanan hoto,

Za a ci gaba da shari'ar Brenton Tarrant, mai shekara 28 bayan sati uku

Wani mutum ya bayyana a gaban kotu a New Zealand inda ake tuhumarsa da laifin kisan-kai kwana daya bayan harin da aka kai na harbi a masallatai biyu a birnin Christchurch, da ya yi sanadaiyyar mutuwar mutane 49.

Brenton Tarrant mai shekara 28 wanda ya bayyana a kotun jami'an tsaro a gefe da gefensa sanye da farar riga ta fursuna da kuma ankwa a hannunsa ya yi wata alama ta fifita farar-fata.

An hana jama'a halartar zaman kotun bisa abin da aka bayyana dalilai na tsaro ko kariya.

Sai nan da sati uku ne za a sake zaman yayin da za a ci gaba da tsare mutumin.

Fira ministar New Zealand, Jacinda Ardern, ta kare zargin da aka yi wa 'yan sandan kasar cewa sun yi jinkiri wajen daukar mataki a lokacin da mutumin ya kai hare-haren, ranar Juma'a.

Ta ce an kama dan bindigar minti 36 bayan samun kiran gaggawa na farko da aka yi, idan da ba haka ba ma da ya so ya ci gaba da harbin.

Jumullar mutane 48 ne aka raunata a hare-haren bindigar, daga cikinsu akwai yara maza guda biyu masu shekara biyu da kuma 13.

Goma sha daya daga cikinsu ana musu magani a asibitin birnin na Christchurch, kuma an ce suna cikin mawuyacin hali in ji babban likitin asibitin Greg Robertson.

Bangladesh da India da Indonesia sun ce akwai 'yan kasashensu da harin ya rutsa da su yayin da wasu kuma babu wani bayani a kansu.

Shugabannin kasashen duniya sun yi allawadai da harin yayin da ake ci gaba da aika sakon jaje da ta'aziyya ga kasar da kuma al'ummar Musulmi.