Kun san Musulman da aka kashe a New Zealand?

Tribute sign at the Botanic Gardens in Christchurch

Mutane 49 ne aka tabbatar da mutuwarsu a ranar Jumma'a bayan wani hari da aka kai a masallatai a birnin Christchurch da ke New Zealand.

Jami'ai a kasar suna aiki tukuru wajen ganin sun samu bayanai dangane da wadanda harin ya rutsa dasu.

Har yanzu babu wanda hukumomi suka bayyana a hukumance a matsayin wanda harin ya rutsa dashi.

Amma lamarin a bayyane yake cewa wadanda aka kashe sun fito daga sassa daban-daban na duniya kuma akasarinsu 'yan gudun hijira ne wadanda suke gani kamar sun samu mafaka zuwan su New Zealand.

Iyalai da dama wadanda har yanzu basu ji daga wurin 'yan uwansu ba suna nan hankalinsu a tashe suna jiran mummunan labari.

Ga wasu daga cikin wadanda aka bada rahoton cewa sun mutu ko kuma ba a gansu ba.

Daoud Nabi, mai shekaru 71

Daoud Nadi shine na farko a cikin wadanda harin ya rutsa da aka fara ganewa.

An haife shi a Afghanistan amma ya yi hijira da iyalensa a shekarun 1980 domin kujewa harin kungiyar Sobiyet a wancan lokaci.

Daoud Injiniya ne kuma masoyin nau'in tsofaffin motoci, amma da ya yi ritaya daga aikinsa ya zama daya daga cikin shugabannin al'ummarsa.

Shine shugaban wata kungiya ta mutanen Afghanistan mazauna New Zealand haka kuma yana goyon bayan kungiyoyi dama na 'yan ci rani.

Sayyad Milne, mai shekaru 14

Sayyad Milne ya so ya zama dan kwallo idan ya girma.

A ranar Jumma'a ya je masallacin Al Noor tare da mahifiyarsa. Mahifinsa ya bayyanawa manema labarai a ranar Asabar a New Zealand cewa: ''Har yanzu ba a bayyana mani a hukumance ya mutu ba amma ya mutu saboda an ganshi.''

''Ina tuna shi a lokacin da yana jariri har na kusan rasa shi a lokacin, yaro ne jarumi. Ina takaici a ce wani da bai san darajar mutane ba ya zo ya harbe shi da bindiga.''

''Nasan inda yake a halin yanzu. Na san Allah ya yi mashi rahama.''

Naeem Rashid

Naeem Rashid asalin dan garin Abbottabad ne a kasar Pakistan. Malamin makaranta ne a Christchurch.

Bayanan hoto,

Naheem Rashid (a hannun dama) tare da 'yanuwansa loakacin wata ziyara

A cikin bidiyon da aka nuno harin da aka kai a masallacin, an ga Naeem Rashid na kokarin kokowa da dan bindigan da yakai harin.

Mista Rashid ya samu rauni sosai, an kai shi asibiti amma iyalensa sun shaidawa sashen Urdu na BBC cewa suna ganin ya mutu. An yabe shi a matsayin jarumi.

Dan uwansa Khurshid Alam ya ce '' tun lokacin muna yara, Naeem yana yawan cewa mutum ya gudanar da rayuwarsa yana taimakon mutane, idan ka mutu mutane za su yabe ka. Duk abinda ya fada ya cika.''

Talha Rashid

Talha shine babban dan Mista Rashid. Yana da shekaru 11 a lokacin da iyayensa suka dawo New Zealand.

Iyalen sun shaidawa sashen Urdu na BBC cewa asibiti sun tabbatar da mutuwarsa.

Bayanan hoto,

Talha Rashid tare da mahaifinsa shekaru kadan da suka gabata

Abokan Talha sun ce ya samu sabon aiki kuma yana shirye-shiryen yin aure a cikin 'yan kwanakin nan.

Wani kawun Talha ya ce ''Kwanaki kadan da suka wuce da na yi magana da Naem Rashid, ya bayyana mani shirye-shiryensa na zuwa Pakistan domin ya zo ya aurar da dansa.''

''Amma a yanzu muna shirye-shiryen kawo gawarwakinsu Pakistan domin birne su.''

Akwai daya daga cikin 'ya'yan Mista Rashid da yana asibiti yana karbar mmagani sakamakon raunukan da ya samu.

Jami'ai a kasar Pakistan basu tabbatar da mutuwar wani dan kasar ba amma ta sanar da cewa akwai 'yan kasar guda biyar da suka bace.

Hosne Ara, mai shekaru 42

Jami'an ofishin jakadancin Bangladesh da ke New Zealand sun ce an kashe mutane uku 'yan kasar Bangladesh sakamakon harin amma ba a bayyana sunayensu ba.

An bayyana cewa Horsne Ara tana bangaren mata a masallacin Al Noor a lokacin da ta fara jin harbin bindiga.

Mijinta mai suna Farid Uddin yana bangaren maza, yana amfani da keken guragu.

Wani daga cikin danginta ya shaida cewa ''tana jin harbin bindiga, ta yi sauri ta taho a guje domin ta ga abinda ke faruwa kuma ta ceci mijinta, a nan ne aka harbe ta da bindiga ta mutu.''

Khaled Mustafa

Wata kungiyar hadin kai ta kasar Siriya da ke New Zealand ta ce an kashe Khaled Mustapha a masallacin Al Noor.

Mista Mustafa dan gudun hijira ne daga Siriya da ya zo kasar New Zealand bayan yakin da aka gwabza a Siriya.

Daya daga cikin 'ya'yan Mustafa har yanzu ba a ganshi ba, daya kuma ya samu raunuka har an yi mashi tiyata.

Mucad Ibrahim, dan shekaru uku

Iyayen wani yaro dan shekaru uku Mucad Ibrahim sun ce basu ganshi ba tun bayan harin da aka kai. Sun duba a asibiti basu ganshi a cikin wadanda ke karbar magani ba.

Dan uwan Mucad mai suna Abdi Ibrahim ya bayyanawa manema labarai cewa Mucad ya mutu.

Ya ce ''Mucad yana da kuzari, yana san wasa kuma yana san murmushi da dariya.''

'Yan sanda sun tabbatar da cewa a kalla yaro daya ne aka kashe aka kuma raunata da dama.

Jami'an basu bayyana sunan kowa ba.

Amjad Hamid, mai shekaru 57

Mista Amjad likita ne mai shekaru 57 wanda ba a kara jin duriyarsa ba tun bayan harin da aka kai a masallaci a ranar Jumma'a.

Iyalensa sun bayyana cewa sun duba asibiti da duk wani wurin da ake tunanin za a iya ganinshi amma basu ganshi ba. Sun ce suna tunanin ya mutu.

Matarsa mai suna Hahan ta bayyana cewa ''abin takaici ne bayan duk shirye-shiryen da muke yi na kyautata rayuwar yaranmu.'' Ta bayyana shi a matsayin mutumin kirki.

Mista Amjad da matarsa sun dawo New Zealand shekaru 23 da suka gabata.

Wani dan kasar Afghanistan da ba a san sunansa da shekarunsa ba

Wata kungiyar 'yan Afghanistan da ke New Zealand ta bayyana cewa akwai wani dan kasar da aka tabbatar da mutuwarsa amma ba a tabbatar da sunansa da shekarunsa ba.

Hussain al-Umari, 35

A duk ranar jumma'a, Hussain yakan je masallaci daga nan ya je gaida iyayensa su ci abincin dare.

Ya yi maganarsa ta karshe da iyayensa a ranar Alhamis. Yana cikin jin dadi saboda sun saya sabuwar mota.

Janna Ezat da kuma Hazim al-Umari wadanda su ne iyayensa sun dawo New Zealand da zama tun a shekarun 1990 daga Hadadiyar Daular Larabawa.

Wadanda ba a sake jin duriyarsu ba an lissafo su daga kasashe da suka hada da Jordan da Indiya da Pakistan da Bangladesh da Afghanistan da Saudi Arabia.

A kalla mutane hudu aka kashe 'yan asalin kasar Somaliya a harin da aka kai.

Daya daga cikin masallatan da aka kai hari ya hada da masalllacin Al Noor wanda da hadin gwiwar 'yan kasar Somaliya ake tafiyar dashi.

Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta wallafa sunayen wadanda aka kashe a shafinta na intanet.

Wadanda suka tsira suna rajistar sunayensu da cewa sun tsira wadanda kuma ba a gansu ba iyalensu na rajistar sunayensu a matsayin wadanda suka bace.