Hatsarin jirgin Ethiopia: An ba dangin mamata turbaya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani Ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya kenan yana juyayin mutuwar abokin aikinsa a inda lamarin ya faru kusa da Addis Ababa

An baiwa iyalan wadanda hatsarin jirgin sama na Ethiopia ya rutsa da su jikkuna dauke da konaniyar kasar wurin da hatsarin jirgin saman ya faru a matsayin gawarwakin 'yan uwansu gabbanin taron addu'oin da za a gudanar a ranar Lahadi a Addis Ababa.

Ana baiwa iyalan na su kilo daya na kasa da za su yi amfani su birne a lokacin taron addu'o'in da za a gudanar.

Daya daga cikin iyalan ya shaida cewa ''dalilin bayar da kasar shine an kasa gane gawarwakin 'yan uwanmu ko kuma kayayyakin su.''

''Baza mu karaya ba sai an bamu ainahin gawarwakin 'yan uwanmu.''

An shaidawa 'yan uwan wadanda hatsarin jirgin ya rutsa dasu cewa za a dauki lokaci mai tsawo kafin a tantance gawarwakin 'yan uwan nasu.

Minstan sufuri na kasar Ethiopia Dagmawit Moges, ya ce gudanar da bincike a kan gano musabbabin abinda ya jawo hatsarin zai dauki masu binciken lokaci mai tsawo.

Ya ce ba abu bane na sauri, sai an bi a hankali an dauki lokaci kafin kammala binciken.

Ana kara ba 'yan uwan wadanda hatsarin jirgin ya rutsa dasu kwarin gwiwar kokarin kai samfarin kwayoyin halitta zuwa ofishin jirgin sama na Ethiopia da ke Addis Ababa ko kuma duk wani ofishinsu da ke fadin duniya.

Ana sa ran fara bayar da takardar shaidar mutuwa nan da mako biyu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyalan wadanda hatsarin ya rutsa dasu na kona kyandir a wurin da hatsarin ya faru

A ranar Lahadi 10 ga watan Maris ne jirgin sama kirar ''Boeing 737 Max'' na kasar Ethiopia ya yi hatsari dauke da fasinjoji 157 da suka fito daga kasashe sama da 30.

Jirgin ya yi hatsarin ne a hanyarsa ta zuwa Nairobi daga Addis Ababa.

Tun bayan hatsarin jirgin, kasashe da dama sun dakatar da amfani da jirgin sama kirar ''Boeing 737 Max.''

Wannan shine karo na biyu da irin wannan samafarin jirgin ya yi hatsari domin kuwa makamancin shi na kasar Indonisiya ya yi hatsari watanni biyar da suka gabata.

Labarai masu alaka