Me zai faru bayan dakatar da amfani da jirgin 737 Max?

The wing of the first Boeing 737 Max airliner, pictured in 2015 Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hatsarin jirgin sama kusan sau biyu da jirgin sama kirar 'Boeing 737 Max' ya yi cikin watanni kadan ya jawo kamfanin jirgin na kokarin dawo da martabarsa a idon duniya.

A lokacin da masu bincike ke gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin, wata hukuma mai sa ido kan sufurin jirgin sama a Amurka ta ce za a dakatar da amfani da samfarin jirgin zuwa a kalla watan Mayu.

Tuni dai kamfanonin da ke sayan jirage daga kamfanin Boeing domin gudanar da sufuri suka fara nuna alamun janye jiki daga hulda da kamfanin na Boeing.

Amma masu sharhi sun bayyana cewa tasirin da kamfanin zai ci gaba da yi nan gaba ya dogara ne bisa rahoton da za a fitar na binciken da ake gudanarwa a halin yanzu.

Kasashe da dama sun dakatar da amfani da samfarin jirgin tun bayan da jirgin Ethiopia kirar 'Boeing 737 Max' ya yi hatsari mintoci kadan bayan ya tashi inda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 157.

Hakazalika a watan Octoban bara jirgin Indonisiya mai suna Lion Air ya yi hatsari wanda shima jirgin kirar 'Boeing 737 Max' ne.

Ya muhimmancin jirgin 737 ya ke ga kamfanin Boeing?

Hukumomi da ke sa ido kan sufurin jiragen sama a Amurka sun bayyana cewa samfarin jirgin da yafi kasuwa a tarihin kamfanin Boeing wato 737, da alamu za a dakatar da amfani da shi har zuwa a kalla watan Mayu.

Jirgin 'Boeing 737 Max' an kera shi ne da sabuwar fasahar zamani kuma an fara sayar da shi a 2017.

A yanzu haka akwai kusan irin wannan samfarin jirgin 370 ana jigila da su a fadin duniya, kuma kamfanin na da kusan jirage 5000 wadanda abokan cinikayya suka bukaci kamfanin ya kera masu.

Wani mai sharhi daga kamfanin jirgi na Teal Group Richard Aboulafia ya bayyana cewa, irin wannan jirgin na 737 Max ba wai yana da girma bane, amma kudin da zai kawo ma kamfanin na da matukar amfani nan gaba.

Ya ce ko wane jirgi kirar 'Boeing 737 Max' ana sayar dashi tsakanin dala miliyan 45 zuwa dala miliyan 50 kuma kamfanin Boeing ya karbi wani kaso na kudi daga hannun abokan cinikayyarsa domin kera masu jiragen.

Ya za a yi da jiragen 737 da aka bayar da kwangilar kera su?

A yanzu haka kamfanin Boeing ya dakatar da kai jiragen da aka bada kwangilar su zuwa ga kamfanonin da suka bada kwangilar kera su bayan umarnin da hukumomi da ke sa ido kan sufurin jiragen sama a Amurka suka bada.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jirgin sama kirar 'Airbus A320 Neo' ne abokin karawar jirgin sama kirar 'Boeing 737 Max' a kasuwar jiragen sama.

Amma duk da haka, wasu daga cikin kamfanonin sufurin da suka bada kwangilar jiragen sama sun bayyana ra'ayinsu na janye kwangilar da suka bada.

Kamfanin jirgi sufurin jirgi na kasar Indonisiya watau 'Garuda Indonesia' ya ce akwai yiwuwar soke kwangilar jirage 20 da ya bayar sai kuma kamfanin 'VietJet' ya ce kwangilar da ya bayar ta dala biliyan 25, binciken da ake gudanarwa zai tabbatar da ko za a janye kwangilar ko baza a janye ba.

Kamfanin sufurin jirgin sama na Kenya shi ma ya ce yana tunanin sauya cinikayyar jirage zuwa kamfanin kera jirgi na Airbus.

Me kamfanonin sufurin jiragen sama ke cewa?

Wasu kamfanonin suna bayyana cewa suna bukatar a biya su diyya.

Kamfanin sufurin jirgi na kasar Norway da kuma na kasar Czech na daya daga cikin wadanda suke kira ga kamfanin Boeing ya biya su diyya.

Amma Mista Aboulafia na kamfanin Teal Roup ya ce Boeing zai iya biyan wannan diyar ba tare da ya girgiza ba.

Ya ce ta kai ta kawo shine kamfanin ya biya daruruwan miliyoyin daloli wanda kuma ba wani abu bane ga kamfanin tunda kamfanin yana samun biliyoyin daloli a duk shekara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu gudanar da bincike a wurin da hatsarin jirgin saman ya faru

Labarai masu alaka