Me ya sa Gwamnatin Kano ta kaddamar da aiki a Gama?

Ayyuka a Gama
Image caption Kwanaki a sake zabe, gwamnati ta kaddamar da ayyuka a Kano

Gwamnatin Kano ta kaddamar da wasu sabbin manyan ayyuka a Gama da ke karamar hukumar Nassarawa inda za a sake gudanar zaben gwamna.

Manyan ayyukan sun hada da shimfida sabuwar kwalta a Gama, mazabar da za ta tantance makomar zaben gwamna a Kano.

Sabbin ayyukan da kuma wadanda aka farfado da su na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a Kano inda wasu ke yaba wa gwamnati wasu kuma ganin an kirkiri ayyukan ne lokaci guda domin janyo ra'ayin mutane don su zabi gwamna Ganduje da ke neman wa'adi na biyu a jam'iyyar APC.

Gama na cikin mazabun da aka soke zabensu sakamakon hari da ake zargin wasu manyan jami'an gwamnati da suka hada mataimakin gwamna sun kai a wajen da ake tattara sakamakon karamar hukumar Nassarawa.

A ranar 23 ga watan Maris ne hukumar INEC ta ce za ta sake yin zabe a wasu mazabu a Kano bayan sanar da cewa ba kammala zaben jihar ba da aka gudanar a ranar 9 ga Maris.

Siyasar Kano na ci gaba jan hankali, saboda girman hamayya tsakanin manyan jam'iyyun siyasa guda biyu APC da PDP da ke yakin lashe kujerar gwamna.

Fafatawar a zaben da za a sake a Kano ta shafi 'yan takarar manyan jam'iyyu biyu ne gwamna Ganduje na APC da kuma babban mai hamayya da shi Abba Kabir Yusuf na PDP.

Jam'iyyun biyu na bin dubaru na janyo ra'ayin jama'a don su zabe su.

Hotunan sabbin ayyuka a mazabun da za a sake zabe a Kano

Image caption Sabon Titin da gwamnatin Kano ke yi daga Kwanar Tudun wada zuwa Unguwar Gama A da C
Image caption Cikin 'yan kwanaki gwamnatin Kano ta fara wannan aikin
Image caption Aikin Kwalta a titin Tudun wada zuwa Gama A da C
Image caption Sama da Shekara guda da fara wannan aikin titin
Image caption Har an shimfida sabon titi cikin 'yan kwanaki
Image caption Aikin Titin zuwa Gama C