'Yan sandan Australia suna sumame kan harin masallaci a New Zealand

policeman stands outside a Christchurch mosque Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan sanda a tsaye bayan harin da aka kai a masallacin Al Noor

'Yan sanda sun kai sumame gidaje biyu a Australia a ci gaba da suke yi na gudanar da bincike kan harin da aka kai a wasu masallatai biyu a Christchurch da ke New Zealand.

Mutane 50 ne suka mutu, da dama kuma suka samu raunuka a harin da aka kai a ranar Juma'a.

Wanda ake zargi da kai harin Brenton Tarran mai shekaru 28 dan kasar Australia, ana ganin kamar ya kai harin ne bisa ra'ayin kansa ba tare da ya hada kai da wasu ko kuma kungiyoyi ba.

An kai samamen ne a safiyar Litinin a gidajen biyu da ke jihar New South Wales a kasar.

Makasudin yin binciken shi ne domin 'yan sanda su samu wata hujja da suke nema domin taimaka wa 'yan sandan New Zealand a kan binciken da suke gudanarwa.

Kafafen yada labarai na Australia sun shaida cewa daya daga cikin gidajen da 'yan sandan suka kai samamen akwai gidan 'yar uwar wanda ake zargi da kai harin wato Mista Brenton.

Firai Ministar New Zealand Jacinda Ardern ta ce za a yi gyara ga tsarin dokar da ta ba da dama a mallaki bindigogi, biyo bayan harin da aka kai a ranar Juma'a.

Mista Brenton da ake zargi da kai harin ya mallaki bindigogi biyar bisa tsarin doka tare da lasisinsu.

Hakazalika, ba a taba samunsa da aikata wani mummunan laifi ba ko kuma a ce 'yan sanda a Australia ko New Zealand suna neman shi ba.

Labarai masu alaka