Me ya sa kasashen yamma ke tsoron kamfanin Huawei na China?

Kamfanin Huawei na daya daga cikin manya ko kuma jiga-jigan kamfanonin fasahar zamani a China kuma shine kamfani na biyu mafi girma da ke wayoyin sadarwa a duniya. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamfanin Huawei na daya daga cikin manya ko kuma jiga-jigan kamfanonin fasahar zamani a China kuma shine kamfani na biyu mafi girma da ke wayoyin sadarwa a duniya

Kamfanin sadarwar na Huawei na daya daga cikin fitattun kamfanonin sadarwa na kasar China da suka yi fice a duniya, amma ko mene ne dalilin da yasa wannan kamfanin ke jawo ce-ce ku ce a kasashen yammacin duniya?

Amurka ta ce dangantakar da ke tsakanin Gwamnatin China da kuma kamfanin Huawei na nuna alamar kokarin da suke yi na mamaye kasuwar network mai karfin 5G da ake kokarin kirkirowa.

Tunanin da Amurkar ta ke yi shi ne kamfanin na Huawei zai taimakawa Beijin tattara bayanan sirri game da kasashen yammaci da kuma kungiyoyi da hukumomin gwamnati.

Washington na daukar kamfanin Huawei a matsayin kamfani mai barazana ga kasa, a wannan dalili ne yasa ta dakatar da kamfanin daga neman kwangiloli na gwamnatin tarayyar kasar.

Shin zargin da ake yi wa kamfanin gaskiya ne?

Kamfanin ya yi ta watsi da zargin da ake yi masa na matsin lamba da gwamnatin China ke yi wa kamfanin na ba ta bayanai inda kamfanin ya kai karar gwamnatin Amurkan yake kalubalantarta a kan dakatar da kamfanin da ta yi.

Wanda ya kirkiro kamfanin na Huawei wato Ren Zhengfei ya shaida wa kafar yada labarai ta CNN cewa Amurka ba ta da kwararan hujjoji da za ta iya gabatarwa kan zargin da take yi wa kamfaninsa.

Ya ce ''kowa a duniya na maganar samar da tsaro ta intanet amma ana kokarin ware Huawei. Kamfanin Sony Ericson fah? Kamfani Cisco kuma fah? Su ba su da matsalolin tsaro a intanet?''

Wannan rashin jituwar na kara kawo fargaba tsakanin China da Amurka a bangaren kasuwanci. A nan, za mu duba bangarori biyar domin duba wannan ce-ce ku cen.

Kutse kan bayanai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Washington na daukar kamfanin Huawei a matsayin kamfani mai barazana ga kasa, a wannan dalili ne yasa ta dakatar da kamfanin daga neman kwangiloli na gwamnatin tarayyar kasar.

Kamfanin Huawei na daya daga cikin manya ko kuma jiga-jigan kamfanonin fasahar zamani a China kuma shi ne kamfani na biyu mafi girma da ke kera wayoyin sadarwa a duniya.

Kamfanin ya sayar da sama da wayoyin sadarwa miliyan 200 a fadin duniya.

Ren Zhengfei yana daya daga cikin 'ya'yan jam'iyyar Chinese Communist Party wacce ita ce jam'iyya mai mulki a kasar China.

Mista Ren injiniya ne na rundunar sojojin kasar China wanda hakan ya ja ake zarginsa a kasashen yammaci da Amurka.

Amurka ta bayyana cewa idan China ta bukaci wani kamfanin kasarta da ya ba ta bayanai da ya samo daga wasu kasashe, lallai za a iya tursasa kamfanin ya bayar da bayanan.

Tun a 2012, kwamitin majalisar tarayya a kan tattara bayanan sirri a Amurka ya bayar da wani rahoto inda yake cewa idan aka bar kamfanin sadarwa na ZTE da kuma na Huawei su yi aiki a Amurka, za su iya kutse kan bayanan sirri.

A shekarar da ta gabata, shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri da Amurka da suka hada da FBI da CIA sun gargadi kasar kan amfani da Huawei da kayayyakin kamfanin.

Kutse ga na'urorin tsaro

Hakkin mallakar hoto Boeing/ Handout

Masana sun bayyana cewa kamfanonin sadarwa za su iya bi ta bayan gida domin samun iko da na'urorin tsaro da sojoji ke amfani da su kamar na'urar da ke harba makami mai linzami.

Ko da kuwa kamfanonin sun samu irin wannan damar ko kuma iko da na'urorin, ba su cika kutse a cikinsu ba saboda za a iya ganewa.

Suna kutse ne kawai idan akwai wani abu da ya taso na gaggawa.

Mista Ren ya musanta cewa hukumomi a China ba su taba bukatar kamfaninsa na Huawei da ya ba su wasu bayanai wadanda suka saba ka'ida ba.

Wani rahoto da kafar yada labarai ta CNN ta fitar ya bayyana cewa kamfanin Huawei na iya kutse ga turakun sadarwa a jihar Montana ta Amurka, domin kawo tsaiko ga yanayin amfani da makami mai linzami da ake amfani da shi a sansanin sojojin sama da ke kusa.

Dokar leken asiri

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kasashen yamma sun damu kwarai dagaske kan wannan dokar

A watan Yulin 2017, China ta yi doka kan leken asiri inda masu sharhi suka bayyana manufar gwamnatin a matsayin wani abu boyayye wanda hakan na nufin tattara bayanai ta ko wane hali.

Kasashen yamma sun damu kwarai da gaske a kan bangare na bakwai na wannan doka inda dokar ta ba da umarnin kungiyoyi da 'yan kasar su taimaka da ba da hadin kai ga hukumar leken asirin kasar wajen samar da bayanai bisa ka'ida.

Amma lauyoyin kasar China sun dade suna kare wannan dokar a kafofin yada labarai na duniya.

Dakta Gu Bin, na jam'iyyar Beijing ya yi rubutu a Jaridar Financial Times inda ya bayyana cewa an yi wa wannan dokar mummunar fahimta kuma dokar ba ta bada damar leken asiri ba.

Amma duk da haka, kamfanin Huawei na fuskantar rashin yarda daga kasashen duniya.

A duk lokacin da kamfanonin China suka gina wani abun more rayuwa a wata kasa, kamfanonin na shan wahala matuka kafin gwamnatocin kasashen su yarda da su.

Yakin cacar baka kan cinikayya

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Duka wadannan ce-ce ku cen na faruwa ne a daidai lokacin da ake samun yakin cacar baka na cinikayyar kasuwanci tsakanin Amurka da China.

A watan Disambar bara lokacin da Shugaban China Xi Jinping da Shugaban Amurka Donald Trump ke tattaunawa a taron kasashe masu karfin tattalin arziki 20 a Argentina, domin tattauna wannan batun yakin cacar bakar, 'yan sanda a Canada sun kama jami'ar hada-hadar kudi ta kamfanin Huawei Meng Xizhou, a filin jirgi na Vancouver.

Meng, wacce diya ce ga Mista Ren, an zarge ta ne da almundahana da kuma kokarin take takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran.

A China, masu sharhi sun bayyana cewa kama ta da 'yan sanda suka yi kamar garkuwa da ita ne.

Sun bayyana cewa kuma har da batun matakan da aka dauka na kasuwanci na cikin shirin da ake yi na saka wa China takunkumi domin dakile kasar daga mamaye tattalin arzkin duniya.

A watan Fabrairun 2018, shugaban wani bangare na kamfanin Huawei Yu Chengdong ya shaida wa BBC cewa ''ko da Amurka ko babu Amurka a kasuwancinmu, kasuwar hada-hadar hannayen jarinmu za ta zama ta daya a duniya.''

Ko da aka tambaye shi dalilin da yasa 'yan siyasar Amurka ba su yarda da kamfanin Huawei ba, sai ya ce: ''Wasu mutane a Amurka suna kokarin dakile mu ta hanyar amfani da siyasa sakamakon gasar da wasu ke yi da mu, mune a gaba wajen kimiyya da fasaha.

Wannan ce-ce ku cen na kamfanin Huawei na kara jawo fargaba tsakanin Amurka da China.