Amurka na keta hakkin dan Adam a Somaliya- Amnesty

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta bayyana cewa hari ta sama da Amurka ta kai a Somaliya ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 14 wanda hakan ya sabawa dokar 'yancin bil adama ta duniya.

Duk da cewa Amurka ta musunta zargin da ake yi mata amma a rahoton da Amnesty International ta fitar, ya bayyana cewa a hari biyar da Amurkar ta kai, an kashe fararen hula 14 da dama kuma sun samu raunuka.

Karkashin mulkin shugaban Amurkar Donald Trump, yakin da Amurkar take yi da kungiyar al-shabab na kara kamari.

A 2018, Amurka ta kai hari ta sama a Somaliya a kalla sau 47.

Amma a wannan shekarar, abin ya wuce haka duk da cewa rundunar sojojin Amurka da ke yaki a nahiyar Afirka wato Africom ta musanta cewa babu fararen hular da aka kashe.

Sai dai kungiyar ta Amnesty ta bayyana cewa tana da hujjoji da suka hada da hotuna da kuma 'yan gani da ido da za su iyar shaidar hakan.

Rahoton na Amnesty ya ce akwai manoma uku 'yan kasar Somaliya da harin ya rutsa da su.

Kungiyar ta ce iyalan wadanda abin ya shafa ba su da wata hanya da za su bi wajen kai karar faruwar lamarin.

Duk da karuwar harin da ake kaiwa al-Shabab, ita ke da iko da akasirin yankunan karkara da ke kudanci da kuma tsakiyar kasar Somaliya

Labarai masu alaka