Duk dan bal na sha'awar Real Madrid - Pogba

Paul Pogba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Paul Pogba ya ce a yanzu yana jin dadin zamansa a Manchester United, amma burin kowane dan wasa ne ya yi Real Madrid

Paul Pogba ya bayyana Real Madrid a matsayin kungiyar da kowane dan wasa zai yi fatan shiga, amma kuma ya ce yana jin dadin zamansa a Manchester United.

Dan wasan na tsakiya mai shekara 26 ya yaba wa kociyansu na rikon-kwarya Ole Gunnar Solskjaer, amma ya ce Real kungiya ce wadda duk wani yaro ko wani dan kwallon kafa yake burin yi.

A wani taron manema labarai a Faransa Pogba ya ce: '' Tana daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya. A kodayaushe ina fadin cewa Real Madrid kungiya ce da kowa ne dan wasa ke fatan taka wa leda.''

Sai dai ganin yana yabon kungiyar ko yana son tafiya can ne, sai ya ce; ''a yanzu dai ina farin cikin kasancewa a Manchester. Ina wasa. Ga kuma sabon kociya.''

Pogba zai buga wa Faransa wasan neman gurbin gasar cin kofin gasar Turai ta 2020 da za su kara da Moldova ranar Juma'a sannan kuma ranar Litinin su fafata da Iceland.

A lokacin da yake tare da tawagar kasarsa, tsohon dan wasan tsakiyar na Juventus ya bai wa dukkanin abokanan wasansa na tawagar Faransa da suka ci Kofin Duniya wani na musamman.

Hakkin mallakar hoto Blaise Matuidi
Image caption Matuidi da Pogba dauke da zoben da dan United din ya sai wa abokan wasansa na Faransa da suka ci Kofin Duniya

Ole ya cancanci a bar masa aikin kociyan Man United

Cigaba da zamansa a Manchester United ya kasance cikin rashin tabbas a lokacin da yake sa-in-sa da Jose Mourinho, wanda Solskjaer ya maye gurbinsa a watan Disamba.

Zuwan Solskjaer kungiyar ya zo daidai da farfadowar dan wasan, wanda ya ci bal hudu a wasansa uku na farko karkashin sabon kociyan.

Kociyan mai shekara 46 ya kulla yarjejeniyar zama a kungiyar har zuwa karshen kakar da ake ciki, amma Pogba ya ce mai horad da 'yan wasan ya yi kokarin da ya kamata a ba shi aikin dindindin.

Pogba wanda yake da kwantiragi da United har zuwa shekara ta 2021 ya ce ''ba shakka muna son ya tsaya''

Ya ce: '' Sakamakon da muke samu yana da kyau. Ina da kyakkyawar alaka da shi. Yana da kyakkyawar alaka da 'yan wasan.

''Idan dan wasa yana jin dadi, yana son a ci gaba da tabbatar da farin cikin nan nasa. Solskjaer ya cancanci aikin. Ya san kungiyar, ya san komai game da kungiyar.

''Kociya ne mai kyau da ke ba wa 'yan wasa kwarin gwiwa. Wannan ne ya sake ba mu 'yancin wasa cikin jin dadi, saboda kila mun rasa wannan saboda irin sakamakon da muke samu a da.''

Lokacin da aka kori Mourinho, United tana matsayi na na shida a teburin Premier, maki 11 tsakaninta da ta hudu, amma yanzu ita ce ta biyar, da tazarar maki uku tsakaninta da Tottenham ta uku.

Haka kuma United din ta kai wasan dab da na kusa da karshe na gasar Kofin Zakarun Turai, bayan da ta doke zakarun Faransa Paris St-Germain.

Pogba ya kara da cewa: ''A yanzu mun fi da kuma sakamakon yana kasancewa mai kyau sosai.''