Jacinda Ardern ta jawo Hadisin Manzon Allah (SAW)

Jacinda Ardern ta jawo Hadisin Manzon Allah (SAW)

Bidiyo daga Reuters

Firai Ministar New Zealand Jacinda Ardern ta jawo Hadisin Manzon Allah (SAW) lokacin taron addu'o'in tunawa da Musulmin da aka kashe a wani masallaci ranar Juma'ar da ta gabata ne.

Ta jawo wani Hadisin da aka ruwaito Annabi Muhammad (SAW) yana cewa "wadanda suka yi imani, masu kyautatawa juna ne da tausayi da jinkai, suna nan kamar sassan jiki daya ne."

"Idan daya daga cikin sassan jikin ya yi ciwo, to sauran jikin ma yana jin zafin ciwon."

Ta ci gaba da cewa: "Kasar New Zealand tana alhini tare da ku, mu da ku abu guda ne."

Har ila yau, kafafen yada labarai a kasar sun sanya kiran sallah da kuma yin shiru na minti biyu don martaba Musulmin da aka kashe a harin masallacin Al-Noor a birnin Christchurch.

Firai Ministar ta je wurin da dubban masu makokin suka taru a kusa da masallacin, wato daya daga cikin wurin da wani mahari ya bude wa Musulmin wuta.

Imam Gamal Fouda, wanda ya jagoranci sallar ya ce: "Mun cikin bakin ciki, amma hakan bai sa mun karaya ba."

Mutum 50 dan bindigar ya kashe, wasu kuma da dama suka ji raunuka.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Imam Gamal Fouda lokacin da yake gabatar da hudubar Juma'a

A ranar Laraba ne aka gawawwakin jana'iza, gabanin a binne su a makabartar Memorial Park Cemetery.