Kwalara ta barke a Mozambique

Yadda ambaliyar ruwa ta cinye gaba ruwan birnin Beira a Mozambique Hakkin mallakar hoto Getty Images

Gamayyar kungiyoyin agaji na Red Cross da Red Crescent sun ce mako guda bayan ambaliyar ruwan da aka samu a Mozambique sakamakon mummunar guguwar da ta afka wa gabar ruwan birnin Beira, an samu bullar cutar amai da gudawa wato kwalara.

Kungiyoyin agajin sun yi gargadi a kan yiwuwar barkewar wasu cutukan kamar yadda uka lura da cewa an samu karuwar wadanda suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro.

Ruwa da iskar dai sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 557 a sassan Mozambique da Zimbabwe da kuma Malawi, amma kuma ana tunanin adadin zai iya karuwa.

Mummunar guguwar ta afka wa birnin ne a ranar 14 ga watan Maris 2019.

Rahotanni sun ce guguwar ta kuma shafi wasu mutum miliyan daya da dubu dari bakwai a sassan kudancin Afirka inda mutanen yankunan suka rasa wutar lantarki da kuma ruwan sha.

Kungiyoyin agajin sun ce ambaliyar ruwan ce ta sanya ruwan shan birnin hadewa da ruwan masai hakan ya sa ruwan ya gurbata abin da ya janyo barkewar cutar t kwalara mai saurin kisa idan ba a gaggauta yi wa wadanda suka kamu magani ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dubban mutane 'yan kasar ta Mozambique sun rasa komai na su, yayin da yara da dama kuma suka rasa iyayensu.

An asarar da dama a kasar da ta hadar da asibitoci da makarantu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akwai akalla mutane dubu 65 da aka tsugunnar a wasu sansanonin wucin gadi 100 wanda yawancinsu ke cikin mawuyacin yanayi.

Labarai masu alaka