Za a yi wa mai nakasar da aka yi wa fyade bulala 100

Inuwar wata mata da aka yi wa fyade a Somaliya

Wani alkali a jamhuriyar Somaliland ya yanke wa wata mata mai lalurar nakasa wacce ta zargi wani mutum da yi mata fyade hukuncin bulala dari.

An yankewa wanda ya yi mata fyaden hukuncin kisa ta hanyar jifa.

Matar dai ta fara kai kara ne ga 'yan sanda a watan Fabrairun 2018. Ta ce wani direban motar tasi ya yi mata fyade a watan Satumbar 2017.

Masu wakiltarta sun shaida wa BBC cewa ba ta kai kara a lokacin da abun ya faru ba saboda ta ji tsoron za a tsangwame ta, amma daga baya ta je ga hukumomi bayan da ta gano cewar tana dauke da ciki.

Sun ce 'yan sanda ba su yadda da labarinta ba saboda lokacin da aka dauka kafin a kai karar cin zarafin da aka yi mata.

Alkalin ya umarci wanda ya aikata laifin ya yi gwajin kwayoyin halitta a lokacin da ya musanta duka zarge-zargen da ake masa.

"Ana cin zarafin mutane da wannan al'umma. Wani irin sako kenan ake aika wa matan da ke son kai karar laifukan da ake masu?" in ji wani lauya mai kare hakkin dan Adam a Somaliland, Guleid Ahmed Jama.

"Har yanzu mata na jin tsoron zuwa wajen 'yan sanda , kuma yanzu da alama ana hukunta su idan suka fito suka bayyana abin da ya same su."

Lauyan da wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam a Somaliland sun daukaka karar kuma suna fatan za a soke hukuncin.

A bara ne sabuwar doka kan fyade da laifukan da suka shafi cin zarafi ta hanyar lalata a Somaliland ta jawo ce-ce-ku-ce a fadin duniya kuma aka ayyana ta a matsayin nasara ga mata.

Mista Jama ya shaida wa BBC cewa a lokacin da aka sa hannu a dokar "mun yi murna amma tuni aka dage dokar kuma ana bita a kanta, babu abin da ya sauya tun da aka sa hannu a kanta".