Ana kammala zabe a jihohi 18

Zaben Najeriya 2019 Hakkin mallakar hoto Getty Images

A jihohi 18 ne za a kammala zabe a ranar Asabar a Najeriya, inda a jihohi biyar ne za a kammala zaben da ya shafi mukamin gwamna da suka hada da Binuwai da Kano da Filato da Sokoto da kuma Bauchi.

A jihar Bauchi, a kananan hukumomi 15 za a kammala zabe a rumfunan da suka kai 36, wadanda ke da adadin kuri'u 22,759.

Wasu wuraren da za a kammala zaben a ranar Asabar sun hada da Bayalsa da Edo da Ebonyi da Ekiti da Imo da Kaduna da Kogi da Osun da Taraba da Legas da kuma Nasarawa da wasu wurare a babban birnin tarayya wato Abuja.

Haka kuma bayan zaben gwamnoni za a kammala zaben 'yan majalisar jihohi.

A ranar 9 ga watan Maris aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisa a fadin Najeriya, inda aka samu takaddama a wasu wuraren.

Hakan ne ya sa hukumar zabe ta tsayar da ranar Asabar mako biyu tsakani domin kammala zabukan da suka zo da takaddamar.