An murkushe daular ISIS a Syria

har yanzu kungiyar na ci gaba da zama barazana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Har yanzu kungiyar na ci gaba da zama barazana

Dakarun Syria na SDF da Amurka ke mara wa baya sun ce daular ISIS mai shekaru biyar ta zo karshe, bayan da aka dakushe mayakanta a kasar Syria.

Mayakan SDF sun yi ta daga tutoci a Baghuz, gari na karshe da masu ikirarin jihadin ke rike da iko.

A lokacin da take kan ganiyarta, kungiyar IS na da iko a kan fadin kilomita 88,000 a fadin Syria da Iraki.

Sai dai duk da kwace iko daga kungiyar, ana tunanin tana ci gaba da zama babbar barazana ga tsaron duniya.

Har yanzu IS na nan a yankin kuma tana da rassa a kasashe da dama kamar Najeriya da Yemen da Afghanistan da kuma Philippines.

Ko yaya fafatawar karshe ta kasance?

Rundunar hadin gwiwa da Kurdawa ke jagoranta ta fara yakinta na karshe da kungiyar IS ne a farkon watan Maris, inda sauran mayakan suka boye a kauyen Baghuz a gabashin Syria.

An tilasta wa hadin gwiwar rage bude wuta bayan da aka gano cewa akwai dimbin fararen hula a garin, zaune a gidaje, rumfuna da wasu maboya a karkashin kasa.

Dubban mata da yara, har da wadanda ba 'yan kasar ba, sun guje wa yakin da rashin abinci da ruwa zuwa sansanonin 'yan gudun hijira da ke karkashin kulawar SDF.

Mayakan IS da dama sun tsere daga Baghuz, amma wadanda suka rage sun dage wajen kunar bakin wake da tayar da bama-bamai a cikin mota.

Shugaban ofishin yada labarai na SDF ya wallafa sako a shafinsa na Twitter inda ya ce "Dakarun Syria sun ayyana kawar da daular gaba daya kuma sun kwato ko wane gari daga kungiyar ISIS."

"A wannan rana mai muhimmanci, mun tuna da dubban shahidai da kokarinsu ya kai mu ga nasara."

A bara ne Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa an yi nasara a kan kungiyar ISIS, kuma ya sanar da shirin dauke dakarun Amurka daga Syria, matakin da girgiza kawayen Amurkar kuma ya sa manyan jami'an gwamnati ajiye ayyukansu.

Sai dai tuni fadar White House ta sanar da cewa za a bar wasu dakarun a yankin.

Me ya sa har yanzu ake ganin IS a matsayin barazana?

IS ta kafu ne daga al-Qaeda a Iraki, bayan da Amurka ta jagoranci yaki a Irakin a shekarar 2003.

Tana cikin wadanda suka yi tawaye ga shugaban Syria Bashar al-Assad a shekarar 2011.

Zuwa 2014, ta karbe yankuna da dama a kasashen biyu (Syria da Iraki) kuma ta yi ikirarin kafa daula.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Karbo ikon Baghuz abu ne mai muhimmanci a yaki da kungiyar IS

Akwai lokacin da IS ta tursasa mulkinta kan kusan mutane miliyan takwas, kuma ta tara biliyoyin daloli daga man fetur da kwace da fashi da garkuwa da mutane, inda ta rika amfani da tasirinta tana kai hare-hare a kasashen waje.

Karbo Baghuz wani babban abu ne a yakin da ake yi da IS. Gwamnatin Iraki ta ayyana nasara kan mayakan a shekarar 2017.

Sai dai da sauran rina a kaba.

Jami'an Amurka suna ganin akwai yiwuwar cewa akwai magoya bayan kungiyar masu rike da makamai 18,000 zuwa 20,000 a yankin.

Duk da dai dakushe kungiyar a Baghuz abu ne mai muhimmanci, IS ta saki wani faifai mai nuna taurin kai inda kakakin kungiyar Abu Hassan al-Muhajir ke tabbatar da cewa daularsu na nan ba a gama da ita ba.

Ba a san inda shugaban kungiyar Abu Bakr al-Baghdadi yake ba. Amma ya kujewa kisa ko kamu duk da ba shi da wuraren buya masu yawa.

Labarai masu alaka