'Yan daba sun hana zabe a galibin garin Gama

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Korafin da wata mata mai zaune a garin Gama ta yi

Ku latsa alamar hoton da ke sama domin sauraran wannan tattaunawar

Wasu 'yan daba dauke da muggan makamai sun yi dirar mikiya kan mazabu daban-daban da ke garin Gama na jihar Kano, inda suka hana gudanar da zabe.

Garin na Gama na da masu zabe kusan 40,000 kuma shi ne wurin da aka fi fafatawa a zaben da ake gudanarwa a karamar hukumar Nasarawa da ke jihar ta Kano.

Wakilan BBC da ke garin sun ga yadda 'yan dabar dauke da makamai suka rika tsorata masu kada kuri'a da kuma korar su.

Har yanzu dai hukumar INEC da kuma rundunar 'yan sandan kasar ba su ce komai dangane da lamarin.

Akasarin mazauna garin sun shaida wa BBC cewa 'yan dabar ba mazauna garin ba ne, suna masu cewa an kawo su ne daga wasu yankunan.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Tattaunawa da wata mata a Gama

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraran wannan tattaunawar

Wakilanmu sun lura cewa jami'an tsaron da aka kai yankin na kallo 'yan dabar na cin karensu babu babbaka ba tare da sun dauki mataki ba.

Mazauna wannan gari sun shaida wa BBC cewa sun firgita sosai inda wasu suka ce sun fasa jefa kuri'unsu domin tabbatar da tsaron lafiyar su.