Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

Zababbun hotuna daga sassan Afirka:

Presentational white space
Ranar Juma'a, masu sha'awar wasan Rugby sun zuba ido suna jiran wasan kungiyar kwallon Rugby ta Afirka ta Kudu ta DHL Stormers da na Jaguares na kasar Argentina. 'Yan Afirka ta Kudun sun ci 35-8 a gida a birnin Cape Town. Hakkin mallakar hoto Gallo Images
Image caption Ranar Juma'a, masu sha'awar wasan Rugby sun zuba ido suna jiran wasan kungiyar kwallon Rugby ta Afirka ta Kudu ta DHL Stormers da na Jaguares na kasar Argentina. 'Yan Afirka ta Kudun sun ci 35-8 a gida a birnin Cape Town.
Yara a babban birnin Kamaru, Yaounde na jiran gamuwa da dan wasan kwallon kafa Samuel Eto'o ranar Litinin a wani taro da FIFA ta shirya. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yara a babban birnin Kamaru, Yaounde na jiran gamuwa da dan wasan kwallon kafa Samuel Eto'o ranar Litinin a wani taro da FIFA ta shirya
Presentational white space
Mako guda bayan faduwar jirgin sama na kasar Habasha, masu alhini sun kunna kyandira don karrama wadanda suka mutu a hatsarin a Addis Ababa... Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mako guda bayan faduwar jirgin sama na kasar Habasha, masu alhini sun kunna kyandira don karrama wadanda suka mutu a hatsarin a Addis Ababa...
'Yan uwan wasu 'yan Kenya da suka mutu a hatsarin jirgin Habasha a ofishin jakadancin kasar a Addis Ababa ranar Asabar... Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan uwan wasu 'yan Kenya da suka mutu a hatsarin jirgin Habasha a ofishin jakadancin kasar a Addis Ababa ranar Asabar...
Duka mutum 157 dake cikin jirgin sun mutu a jirgin Ethiopian Airlines mai lamba ET302 minti 6 da tashinsa daga Addis Ababa. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Duka mutum 157 da ke cikin jirgin sun mutu a jirgin Ethiopian Airlines mai lamba ET302 minti shida da tashinsa daga birnin Addis Ababa
Presentational white space
Dubban 'yan Algeriya 'yan shekaru daban-daban sun fito zanga-zangar da ake yi ta nuna kin jinin Shugaba Bouteflika, ciki har da wannan yarinyar a birnin Paris ranar Lahadi. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dubban 'yan Algeriya 'yan shekara daban-daban sun fito zanga-zangar da ake yi ta nuna kin jinin Shugaba Bouteflika, ciki har da wannan yarinyar a birnin Paris ranar Lahadi
Presentational white space
Ranar Laraba, kwanaki biyar bayan mahaukaciyar guguwar Idai ta afka birnin Beira a Mozambique, wutar lantarki ta dauke gaba daya. 'Yan kasar 500,000 ba su da wutar lantarki da layin waya... Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar Laraba, kwanaki biyar bayan mahaukaciyar guguwar Idai ta afka birnin Beira a Mozambique, wutar lantarki ta dauke gaba daya. 'Yan kasar 500,000 ba su da wutar lantarki da layin waya...
Mahaukaciyar guguwar ta wuce ta Zimbabwe, inda ta shafi mutane 200,000. Wannan titin a yankin gabashi na Chimanimani ranar Litinin ya dauke ya bar ma'aikata a halin ka-ka-ni-ka-yi... Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahaukaciyar guguwar ta wuce ta Zimbabwe, inda ta shafi mutane 200,000. Wannan titin a yankin gabashi na Chimanimani ranar Litinin ya dauke ya bar ma'aikata a halin kaka-ni-ka-yi...
Wannan iyalin 'yan Beira na cikin wadanda suka tsere wa guguwar. Ana tunanin guguwar Idai ta hallaka mutane 300 a Mozambique da Zimbabwe da Malawi. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan iyalin 'yan Beira na cikin wadanda suka tsere wa guguwar. Ana tunanin guguwar Idai ta hallaka mutane 300 a Mozambique da Zimbabwe da Malawi.
Presentational white space
A arewacin Masar, wani manomin alkama na yi wa shukarsa feshi da maganin kwari da asuba. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A arewacin Masar, wani manomin alkama na yi wa shukarsa feshi da maganin kwari da asuba.

Hotuna daga AFP da Getty Images da Gallo Images

Labarai masu alaka