Tambuwal ya lashe zaben Sokoto

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Hakkin mallakar hoto TAMBUWAL/FACEBOOK

Dan takarar jami'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya lashe zaben Sokoto da kuri'u 512,002, bayan da ya doke Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC.

Ahmed ya samu kuri'u 511,660 inda Tambuwal ya tsallake rijiya da baya da bambancin kuri'u 342.

A zaben da aka kammala a ranar Asabar, APC ta samu kuri'u 25,515 sai kuma jam'iyyar PDP wadda ta samu kuri'u 22,444.

A yanzu haka dai Aminu Tambuwal ne ya lashe zaben da aka kammala.

Ranar Asabar 9 ga watan Maris ne aka gudanar da zabukan gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi a Najeriya.

Kuma an samu tsaiko a wasu jihohi inda sakamakonsu bai kammalu ba, kuma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da kammala karashen zaben ranar 23 ga watan Maris din.

Jihar Sakkwato na daya daga cikin jihohin da zabensu bai kammalu ba saboda gibin da ke tsakanin 'yan takarar biyu bai kai yawan kuri'un da aka soke ba, inda aka soke zabe a rumfunar zabe 135 da kusan kuri'u 75,000.

Gwamna Tambuwal dai ya nemi wa'adi na biyu ne inda ya doke tsohon mataimakinsa Ahmed Aliyu wanda APC ta tsayar dan takararta kuma wanda tsohon gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko ke mara wa baya.