Shin laifi ne zana hoton shugaban kasa?

Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi

Masu amfani da shafukan sada zumunta na nuna goyon bayansu ga wasu dalibai mata 'yan kasar Burundi da ke fuskantar dauri, bayan da suka zana hoton shugaban kasarsu a littafansu na makaranta.

Masu amfani da shafukan sada zumunta na Twitter dai na amfani ne da maudu'in #FreeOurGirls wato 'a sako mana 'yan matanmu', ta hanyar yada hoton Shugaba Pierre Nkurunziza da aka zana hular gashi da gashin baki da malafa a kai.

Kungiyar Human Rights Watch mai kare hakkin dan Adam ta ce an kama 'yan matan uku ne makonni biyu da suka wuce kuma suna sauraren shari'a ne bayan da aka tuhume su da zagin shugaban kasar a makon jiya.

Kungiyar ta kuma ce da farko hukumomi sun kama 'yan makarantar bakwai ne, amma an saki hudu daga cikinsu jim kadan bayan kama su.

Sauran ukun, 'yan shekaru kasa da 18 na tsare a gidan yari.

A makon jiya ne, shugaban kungiyar Human Rights Watch a yankin Tsakiyar Afirka, Lewis Mudge ya ce mahaifin daya daga cikin daliban mata ya ce daliban sun kasa cin abinci saboda tsananin tsoro.

Mista Mudge ya kara da cewa: "Abin takaici ne a a ce an kama kananan yara saboda abin da bai kai ya kawo ba duk da irin manyan laifukan da ake aikatawa a Burundi.

"Ya kamata hukumomi su mayar da hankali wajen kama masu aikata manyan laifuka maimakon kama 'yan makarantar don kawai sun yi zane."