Kotu ta amince a tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa

INEC Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kotun tarayya da ke Abuja ta sauya matsayarta kan hukuncin da ta dauka kan dakatar da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, inda yanzu haka ta amince da ci gaba da tattara sakamakon zaben.

A baya dai kotun ta saurari karar da dan takarar jam'iyyar APC a jihar Gwamna Mohammed Abubakar ya shigar inda ya bukaci a dakatar da hukumar INEC daga tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa.

Alkalin kotun ya yai watsi da batun lauyan dan takarar wato Mista Ahmed Raji, inda ya bukaci a dakatar da tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa.

A hukunci da alkalin ya yanke a baya, Mista Inyan Ekwo ya ba bangarorin biyu umarnin tsayawa yadda suke har sai kotun ta yi hukuncinta.

Alkalin ya bayyana cewa karar da aka shigar a gaban kotun kara ce da ta danganci zabe kuma kotun sauraren karar zabe wato Electoral Tribunal kadai ce za ta iya yanke hukunci kan wannan batun.

Tun da farko dai Lauyan dan takarar APC ya bayyana cewa kotun sauraren karar zabe ta na sauraren kara ne kawai bayan an bayyana sakamakon zabe, a cewarsa karar da ya shigar a yanzu ta kunshi abubuwa ne da suka faru kafin bayyana sakamakon zabe.

A yanzu haka dai kotun ta ba hukumar zaben cikkakiyar damar ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar.

A ranar Talata ne dai kotun ta dakatar da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa a lokacin da hukumar ke dab da fara tattara sakamakon zaben.

Tuni dai aka kammala zaben a kananan hukumomi 15 din da aka dakatar da zaben su sakamakon matsalolin da aka fuskanta.

Tun bayan kammala zaben, hukumar INEC ta kammala tattara sakamakon zaben jihar inda na karamar hukumar Tafawa Balewa ne ya yi saura.

A yanzu haka dai an kammala zabe a duka kananan hukumomi na jihar Bauchi bayan hukumar ta soke zaben wasu kananan hukumomi a baya.