Ra'ayoyin jama'a kan zaben Kano
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayoyin jama'ar Kano kan zaben gwamnan jihar Kano

Latsa hoton da ke sama domin kallon ra'ayoyin jama'ar Kano.

Tun bayan kammala zaben jihar Kano, jama'a da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan yadda zaben ya gudana.

Wasu daga cikin 'yan jihar sun amince da sahihancin zaben, wasu kuma sun bayyana akasin hakan.

Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC neya lashe zaben gwamna a jihar Kano a wa'adin shugabanci na biyu, kamar yadda hukumar zabe (INEC) ta bayyana ranar Lahadi.

Ganduje ya kayar da Abba Kabir Yusuf dan takarar babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, bayan sanar da sakamakon zaben jihar da aka kammala a ranar Asabar 23 ga watan Maris.

Gwamna Ganduje ya lashe zaben ne da tazarar kuri'a 35,637 inda jam'iyyarsa ta APC ta samu kuri'a 45,876 yayin da PDP ta samu 10,239.

Yanzu jimilla, APC ta samu kuri'a 1,033,695, yayin da PDP ta samu jimilla 1,024,713. Hakan na nufin Ganduje ya lashe zaben ne da tazarar kuri'a 8,982.

Sai dai jam'iyyar PDP reshen Kano ta yi watsi da sakamakon zaben na gwamna da aka kammala.