An wanke Trump bisa zargin laifin murde zabe

Trump ya dade yana musanta cewa bai hada hannu da Rasha ba domin murde zaben kasar a 2016 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Trump ya dade yana musanta cewa bai hada hannu da Rasha ba domin murde zaben kasar a 2016

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa rahoton mai bincike na musamman Robert Mueller ya wanke shi daga zargin da ake yi masa na sa hannu wajen murde zaben kasar a 2016.

Rahoton wanda aka dade ana jiransa ya bayyana cewa kungiyar yakin neman zaben shugaba Trump ba ta hada hannu da Rasha ba domin murde zaben ba.

Amma rahoton bai bayyana ba ko Trump ya yi kokarin hana bincike ko katsalandan a shari'ar ba.

Zargin murde zaben ya zama wani babban kalubale kan shugaban inda hakan ke yi masa barazana bisa sake zabensa a 2020.

'Yan majalisa daga jam'iyyar Democrats na neman a basu cikakken bayani kan rahoton ba wai tsakure ba kamar yadda ministan sharia'r kasar ya yi masu a baya inda bai fito ya yi masu cikkaken bayani ba.

Mai magana da yawun fadar White House, Sarah Sanders ta bayyana cewa shugaba Trump zai ba Mr Barr damar yin abin da ya ga dama, amma zai yi farin ciki idan aka saki dukkanin rahotan.

Image caption Wasu makusantan shugaba Trump da kotu ta kama da laifi kan hada hannu da rasha wajen murde zaben kasar na 2016

Shugaba Trump a filin jirgin kasa na Florida ya bayyana cewa " babu wani hadin baki da Rasha ko kuma katsalandan a shari'a, an wanke (ni) daga wannan.

Labarai masu alaka