Kotu ta ba da umarnin kammala zabe a Adamawa

Takardar jefa kuri'a Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wata kotu a Adamawa ta sauya matsayarta bisa umarnin da ta bayar na dakatar da kammala zaben gwamna a jihar Adamawa, inda a yanzu haka ta bayar da damar kammala zaben gwamna a jihar.

Kotun ta zartar da sabon hukuncin na ta ne a ranar Talata bayan dan takarar jam'iyyar MRDD Reverend Eric Theman ya shigar da kara bisa kuskuren da aka samu na kin sa alamar jam'iyyarsa kan takardar jefa kuri'a.

Karar da dan takarar ya shigar a kotun ya sa hukumar INEC ba ta gudanar da zaben cike gibin da aka gudanar a sauran jihohi biyar a Najeriya ba.

A yanzu haka hukumar INEC a Najeriya ta karbi hukuncin da kotun ta zartar domin tuni ta wallafa shi a shafinta na Twitter.

Hukumar ta ce za ta kammala zaben ne a ranar Alhamis.

Tun a baya jihar Adamawa na daga cikin jihohi shida da hukumar INEC din ta bayyana zabensu a matsayin wanda ba a kammala ba.

A ranar 11 ga watan Maris ne baturen zaben jihar ta Adamawa Farfesa Andrew Haruna ya bayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammala ba, sakamakon yawan kuri'un da aka soke kusan 40,000 sun fi tazarar da ke tsakanin 'yan takarar PDP da APC yawa.