A binciki harin da aka kai wa ma'aikatan BBC a Kano – Amnesty

Ma'aikatan BBC ya yin da aka ceto su bayan harin da aka kai masu
Image caption Ma'aikatan BBC yayin da aka ceto su bayan harin da aka kai masu

Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomi a Najeriya da su yi bincike kan harin da 'yan daba suka kai wa 'yan jarida a lokacin zaben cike gibi a mazabar Gama a jihar Kano.

Kungiyar ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter inda ta bayyana cewa akwai zargin da ake yi wa wasu 'yan siyasa masu "alaka da gwamantin jihar Kano" da hannu wajen kai hari ga ma'aikatan BBC Hausa da kuma gidan talabijin na TVC.

Sai dai gwamnatin jihar ta musanta zargin kuma jami'an tsaron kasar ba su ce komai ba tukuna.

Kungiyar ta ce ya zama dole masu hannu kan wannan lamarin shari'a ta yi hukunci a kansu.

A ranar Asabar ne dai wasu 'yan daba suka afka wa 'yan jaridar a daidai lokacin da suke hada rahotanni dangane da zaben da ake kammalawa a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.

Wakilan BBC da lamarin ya rutsa da su sun shaida cewa sun sha da kyar, domin sai da aka turo jami'an tsaro suka ceto su, bayan sun samu mafaka an boye su a mazabar ta Gama.

Wasu sun yi zargin cewa lokacin da aka gudanar da zaben cike gibin, 'yan daba dauke da makamai suka rika tsorata masu kada kuri'a da kuma korarsu wanda hakan ya jawo jama'a da dama ba su jefa kuri'a ba a wasu rumfuna a mazabar Gama.