Rundunar Sojin Algeriya sun bukaci a cire Shugaba Abdelaziz Bouteflika

Abdelaziz Bouteflika Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Shugaba Abdelaziz Bouteflika ya karbi mulkin kasar ne shekara 20 da suka wuce

Shugaban rundunar sojojin kasar Aljeriya ya bukaci da a ayyana shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika a matsayin mara lafiya, wanda ba zai iya jan ragamar mulkin kasar ba.

Da yake magana ta kafar talabijin din kasar Laftanal Janar Ahmed Gaed Salah ya ce: "ya zama dole mu gaggauta nemo bakin zaren rikicin nan ta hanyar doka."

Laftanal Janar din ya bukaci da a yi amfani da sashe na 102 na kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya bayar da dama a ayyana babu shugaban kasa yayin da shugaban ba shi da lafiya, ko ba zai iya mulki ba.

Tun a baya dai shugaban ya bayyana cewa ba zai yi takara ba a karo na biyar a zabukan da ke tafe wadanda aka jinkirta.

Sai dai duk da haka wasu 'yan kasar sun ci gaba da zanga-zanga tare da zargin shugaban mai shekara 82 da yunkurin tsawaita wa'adin mulkinsa.

Tsoma bakin da shugaban sojojin ya yi shi ne ci gaba na baya-bayannan da aka samu bayan makonni da aka shafe ana zanga-zanga a kasar.

Labarai masu alaka

Karin bayani