Wadanne kalubale ne ke gaban El-Rufai?

Hakkin mallakar hoto TWITTER/NASIR ELRUFA'I

Nasir Ahmad El-Rufai ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna a karo na biyu, bayan fafatawar da yayi da abokin hamayyarsa Isa Ashiru Kudan na jam'iyyar PDP.

El-Rufai ya sami wannan nasara da kuri'u 1,044,710, inda ya bai wa Ashiru tazarar kuri'u sama da 200,000.

Duk da cewa gwamnan ya sha bayyana cewa lashe zaben a 2019 bai dada shi da kasa ba, illa kawai Allah ya zaba wa jihar wanda zai tabbatar da ci gaba, magoya bayansa sun ci gaba da nuna cancantarsa a duk lokacin da suka sami dama.

To a yanzu da yayi nasarar lashe zaben, ko wadanne kalubale ne ke gabansa?

Matsalar Tsaro

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jihar Kaduna jiha ce mai matukar rarrabuwar kawuna, ganin cewa an yi raba dai-dai tsakanin Kirista da Musulmi a jihar, kuma tana da kabilu da dama. Domin haka ta na da tarihin rikicin addini da kabilanci.

Tun a shekarun 1990, jihar Kaduna ta fuskanci tashe-tashen hankula da suka yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da rasa dukiyoyin da darajarsu ba sa misaltuwa.

Duk da cewa rikice-rikicen addini da na kabilanci sun ragu sosai musamman a cikin kwaryar garin Kaduna a yanzu, a kauyuka kuwa har yanzu ana samun aukuwarsu, musamman ma a kauyukan da ke kudancin jihar.

A baya, gwamnan ya taba barazanar tayar da garin Gonin Gora da ke kusa da birnin Kaduna dungurungun saboda kaurin suna da matasan garin suka yi na tayar da husuma.

Haka kuma akwai matsalar garkuwa da mutane da kusan yanzu ta zama ruwan dare a ciki da wajen garin.

Matsalar garkuwa da mutane ta jefa mutane da yawa cikin fargabar zuwa Kaduna musamman ma ta hanyar Abuja da Birnin Gwari.

Sau da yawa idan wani ya ce zai je Kaduna, ko ma Kano a kan ce ma sa "Amma dai ba da mota za ka je ba ko?"

Wannan ya sa jama'a da dama suka koma amfani da jirgin kasa domin gudun abin Allah kyauta da zai iya faruwa da su a hanyar.

Wannan ya nuna hatsarin da ke tattare da hanyar da kauyukan da ke kan hanyar.

Karasa ayyukan da aka fara

A lokacin da ya hau mulki a wa'adinsa na farko, El-rufai ya soma ayyuka gadan-gadan kamar shimfida tituna cikin unguwannin Kaduna.

An kammala da yawa daga cikin wadannan titunan, amma har yanzu akwai wadanda ba a gama ba kamar titin da ya ratsa wani yanki na birnin Kaduna mai suna Unguwar Dosa.

Kafin zabe ma wasu sun rika ganin kamar gwamnan zai fadi saboda wadannan ayyukan da ba a kammala ba a shekaru hudu.

Sai dai ayyukan sun samu cikas ne saboda kin amincewar da wasu sanatocin jihar suka yi na karbo bashin dala miliyan 350 daga Babban Bankin Duniya da gwamnatin El-rufa'i ta gabatar.

Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa gwamnan ya samu matsala da wadannan sanatocin da ke wakiltar Kaduna a majalisar dattawan Najeriya a baya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sai kuma aikin ruwan sha a birnin Zaria, wanda jim kadan bayan hawan gwamna El-Rufai ne ya sanar da cewa ya kammala zangon farko na aikin.

Har yanzu wasu daga cikin jama'ar Zaria basu fara ganin ruwan sha na kwarara daga famfunansu ba da tuni tsa-tsa ta cinye su.

Hada kan al'ummar jihar

Jihar Kaduna jiha ce mai al'ummomi daban-daban da ke zaune tare da juna.

Ana iya cewa Jihar ta kasu gida biyu, inda mafi yawan mutanen da ke yankin arewacin jihar Hausawa ne yayin da sauran kabilun ke zaune a yankin kudancin jihar.

Jihar ta Kaduna cike ta ke da mabiya addinan Musulunci da na Kirista.

Akwai manyan malaman Musulunci da na Kirista da ake takama da su a fadin Najeriya da ke zaune a cikin jihar.

Amma duk da haka, an samu rarrabuwar kawunan al'ummar jihar; musamman ma a lokacin zaben 2019 sakamakon nuna bambanci na kabilanci da na addini.

Babbar shaidar hakan ita ce yadda a lokacin zaben gwamna taswirar jihar Kaduna ta rabu biyu inda yawancin mutanen kudancin jihar suka zabi PDP, na arewacin jihar kuma suka zabi APC.

A yanzu haka hadin kan al'ummar jihar na daya daga cikin abubuwan da ya kamata gwamnan ya sa a gaba domin kawo zaman lafiya da kuma ci gaba.

Muddun aka ce al'umma kanta ba a hade yake ba, duk na'uin ci gaban da aka kawo cikinta ba zai yi karko ba.

Dawo da martabar ilimi a jihar

Akwai matakai da gwamnan ya dauka na dawo da martabar ilimi a jihar musamman na firamare da ba su yiwa jama'ar da dama dadi ba wasu kuma na ganin daukar wadannan matakan su ne daidai.

Matakan sun hada da tantancewa da korar malamai da kuma ciyar da daliban jihar abinci.

Bisa binciken da gwamnan ya yi, ya bayyana cewa da dama daga cikin malaman makarantar firamare na jihar ba su cancanta su koyar ba.

A wannan dalilin ne ya sa aka tasa keyar sama da malaman firamare dubu 24 a jihar wanda wasu na ganin hakan ya dace wasu kuma na ganin bai dace ba.

Koma dai ya yi daidai ko bai yi daidai ba aikin gama ya gama, babban kalubalen da ke gaban gwamnan shi ne a tabbatar da sabbin malaman da za su koyar a matakin firmare za su iya kai daliban ga tudun mun tsira a bangaren ilimi.

A bangaren ciyar da dalibai abinci kuma, gwamnan ya kawo wannan shirin idan ba a manta ba tun a farkon hawan shi mulki.

Wasu 'yan jihar sun yi ta sukar wannan mataki inda suke ganin asarar kudi ne wasu kuma na ganin ci gaba ne ga jihar ganin cewa da dama daga cikin daliban sun fito ne daga gidajen marasa galihu.

Kalubalen da ke gaban gwamnan kan wannan lamarin shi ne sake duba tsarin ciyar da daliban, bayan korafe-korafen da iyayen yara da kuma jama'ar jihar ke yi.