Isra'ila ta kai hari zirin Gaza

Taswirar kasarIsra'ila da ta Falastinu
Image caption Taswirar kasar Isra'ila da ta Falastinu

Hukumar dakarun Isra'ila (IDF) ta yi ruwan bama-bamai a zirin Gaza bayan da wasu mayaka suka harba wasu rokoki cikin kasar.

Dakaraun kasar Isra'ila din sun bayyana cewa sun kai hari ne a ofishin shugaban kungiyar Hamas da kuma ofishin binciken sirri na kungiyar.

Hukumar kula da lafiya ta Gaza ta bayyana cewa mutane bakwai sun jikkata sakamakon harin.

Bayan tsagaita wuta na wani lokaci sai mayakan suka sake harba wasu rokoki zuwa cikin Isra'ila wanda hakan ya jawo martani daga kasar.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin harba rokokin inda daya rokar ta fada a wani gida a Mishmeret, kudancin Tel Aviv a ranar Litinin.

Sojin Isra'ila sun zargi Hamas da harba rokokin inda wani babban jami'in Hamas ya musanta zargin.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu kidaden da harin dakurun Isra'ila suka ruguza

Wannan na zuwa ne bayan da aka kwashe makonni ana takaddama tsakanin sojojin Isra'ila da masu zanga-zanga a iyakar kasashen guda biyu.

Wannan na zuwa ne makonni biyu na lokacin da za a yi zabe a kasar Isra'ila.

Labarai masu alaka