INEC ta fasa ba 'yan takara shaidar cin zabe a Zamfara

Mahmud Yakubu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jam'iyyar ta APC ba ta san makomarta ba a Zamfara har sai da ya rage kasa da mako daya kafin zaben gwamnoni

Hukumar zabe ta kasa INEC ta dakatar da bai wa 'yan takara da suka yi nasara a zaben gwamna da na 'yan majalisar jiha a jihar Zamfara takardar shaidar nasarar cin zaben, wato Certificate of Return.

Wannan ya biyo bayan wani umarni ne da hukumar ta ce ta samu daga wata kotu a birnin Sokoto game da rikicin jam'iyyar APC da ke da alaka yadda aka yi zaben fitar da gwanin da suka yi mata takara a jihar.

Hukumar ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter, inda ta ce tana ci gaba da nazari kan umarnin kotun.

Tun farko dai INEC din ta sanya ranar Laraba 27 ga watan Maris a matsayin ranar da za ta gabatar wa da dan takarar APC Alhaji Mukhtar Shehu Idris shaidar lashe zaben gwamna da kuma 'yan majalisar jiha da suka yi nasara a zaben da aka kammala.

Yanzu dai hukumar ta ce ta dage bai wa 'yan takarar shaidar, har sai wani lokaci nan gaba da ba ta bayyana ba.

Jam'iyyar APC dai a jihar Zamfara na fama da rikici tun bayan zaben fitar da gwani da ta gudanar kafin babban zaben da aka gudanar a Najeriya.

A ranar Litinin ne wata kotu ta soke hukuncin wata kotun daban a kan 'yan takarar APC din na jihar.