Gudaji Kazaure on NASS Leadership
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gudaji Kazaure: Mu da muka yi wahala ya kamata mu jagoranci majalisa

Ku latsa alamar lasifikar da ake sama don sauraron hirar:

Batun shugabancin majalisa ya fara raba kan 'ya'yan jam'iyyar APC a Najeriya inda wasu suka ce suna adawa da tsarin ware mukami ga wata shiya.

Hon Gudaji Kazaure daya daga cikin masu neman kujerar kakakin majalisar wakilai ya nuna baya goyon bayan kebe mukami ga wata shiyya illa a baje a faifai mai rabo ya samu.

Dan majalisar ya shaida wa BBC cewa yana nan kan bakarsa ta neman kujerar kakakin majalisar wakilai kuma zai nemi goyon baya daga 'yan uwansa 'yan majalisa domin su zabe shi.

Jam`iyyar APC da ke da rinjaye na neman hada kan 'ya'yanta ne don mamaye dukkan manyan mukaman da ke sabbin majalisun dokokin da za a kafa, kasancewarsu masu rinjaye.

APC na son kaucewa barakar da ta samu a shekara ta 2015, inda jam`iyyar hamayya ta PDP ta shammace ta har ta mamayi kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Hon Gudaji Kazaure ya ce ya ja kunnen APC cewa idan ba a yi hattara ba abin da ya faru a 2015 yana iya sake faruwa a bana.

Ya yi kira ga shugaban kasa Buhari ya diba magoya bayansa irinsa wadanda ba za su bari a saba ma shi ba.

"Ba yanda za a yi ace an ci yaki an yi nasara amma idan an zo kason ganima ace ba za a fara duba wadanda suka fi shan wahala da yin biyayya," in ji shi.

Ya kara cewa ya kamata a duba a ga wadanda suka fi jajircewa a ba su shugabancin majalisa.