Kamfanin Boeing ya ce ya gyara manhajar jirgin 737 Max

Debris from Ethiopian Airlines flight 302 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Debris from Ethiopian Airlines flight 302

Boeing ya sanar da jerin sauye-sauyen da zai yi wa na'urorin jrgin nan samfurin 737 Max 8 wanda sau biyu yayi hadari cikin wata biyar.

Amma babu wanda ya san lokacin da jiragen za su koma bakin aiki tun bayan da aka dakatar da ilahirin samfurin jirgin a fadin duniya.

Masu bincike ba su gano dalilan da suka sa jirgin ya rika rikitowa ba kawo yanzu.

Cikin sauye-sauyen, Boeing zai saka wa jiragen wata manhaja da za ta rika yi wa matukansa gargadi da zarar wata matsala wajen tashi ta auku.

Kafin yanzu dai wannan tsarin ana saka wa jiragen ne idan wadanda suka mallaki jirgin sun bukaci haka.

Dukkan jirage biyu da suka yi hadari, wato na kamfanin Lion Air na Indonisiya da kuma na Ethiopian Airlines ba su da wannan manhajar.

Kamfanin na Boeing ya ce daga yanzu ba zai sake neman kamfanonin jigilar fasinja su rika biyansa kudade ba domin a saka masu wannan manhajar.

Hakkin mallakar hoto Boeing
Image caption babu wanda ya san lokacin da jiragen za su koma bakin aiki

Labarai masu alaka