Zaben shugaban Majalisar Dattijai na iya jawo baraka a APC - Masana

Sanata Ahmed Lawan Hakkin mallakar hoto @SenAhmadLawanI

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kebe shugabancin majalisar dattawa ga shiyyar arewa maso gabashin kasar tare da bayyana sunan wanda take so ya kasance shugaba.

Sanata Ahmed Lawan ne daga jihar Yobe jam'iyyar ta zaba a matsayin wanda take son ya zama shugaban majalisar dattawa.

APC ta ce ta yanke wannan hukunci ne na zabar Sanata Ahmad Lawan ya jagoranci majalisar dattawa da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari da manyan jiga-jiganta.

Amma batun shugabancin majalisun dokokin kasar na neman zame wa jam'iyyar APC da wasu 'ya'yanta alakakai.

Wasu daga cikin 'yan majalisar sun ce hakan ba adalci ba ne, kamata ya yi a bar masu son mukamin su yi takara, amma jam'iyyar ta ce ba za ta sauya matsayinta ba.

Majiyoyi sun ambato Sanata Ali Ndume daga shiyar arewa maso gabashi na bayyana adawa da zabin uwar jam'iyyar, inda ya ce kamata ya yi a bar sanatocin shiyar su baje a faifai maimakon jam'iyyar ta nuna inda ta karkata.

Masu sharhi dai na ganin matakin da jam'iyyar ta dauka na iya zama babbar baraka da za ta kai ga raba 'ya'yanta a majalisa kamar yadda ta faru a 2015.

Farfesa Jibril Ibrahim na cibiyar bunkasa dimokuradiyya a Najeriya ya ce ana iya shiga rikici tun kafin ma a fara aiki a majalisar.

Ya ce 'ya'yan jam'iyyar za su iya rabuwa kashi biyu, wasu su goyi bayan zabin jam'iyyar wasu kuma su bijere su zabi wani dan takarar.

APC na son kaucewa barakar da ta samu a shekara ta 2015, inda jam`iyyar hamayya ta PDP ta shammace ta har ta mamayi kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Sai dai wasu na ganin har yanzu jam'iyyar na iya fada wa tarkon da ta fada a 2015.