Brexit: Theresa May ta yi tayin yin murabus

Theresa May speaking in the Commons on 27 March Hakkin mallakar hoto UK Parliament/Mark Duffy

An kasa samun masalaha a majalisar Birtaniya kan yadda kasar za ta fice daga Tarayyar Turai.

Bayan kasa samun nasara sau biyu kan yarjejeniyar da Firai Minista Theresa May ta amince tsakaninta da Tarayyar Turai, 'yan majalisa sun kada kuri'a amma kuma babu daya daga cikin zabi takwas da ya samu rinjaye a ranar Laraba.

Kuma a yayin da manyan masu goyon bayan ficewar Birtaniyar daga Tarayyar Turai suke sake goya wa yarjejeniyar Theresa May baya, su kuwa 'yan majalisar da ta dogara kan samun goyon bayansu na jam'iyyar DUP sun ki su sauya matsayarsu.

Firai Ministar ta shaida wa 'yan majalisa daga jam'iyyarta ta Conservative cewa za ta yi murabus idan har majalisa ta amince da yarjejeniyarta ta ficewa daga Tarayyar Turai.

Hakan na nufin za ta iya sake gabatar da shirinta ga 'yan majalisar dokokin a wannan makon don a sake kada wata kuri'ar - daga kuri'a ta uku da za a kada wadda ta ke fatan gabatarwa nan da kwanaki biyu masu zuwa, bayan kayen da ta sha a kuri'u biyun da aka riga aka kada.

Babban abokin Misis May kuma tsohon mataimakinta Damian Green ya shaida wa shirin BBC Radio 4 na ranar Alhamis cewa firai ministar "za ta ci gaba da yunkurin fitar da kasar daga Tarayyar Turai."

Amma duk da cewa firai ministar ta samu nasara kan mutane irin su tsohon sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson, wasu 'yan gaba-gaba a shirin ficewar kasar daga EU sun ki amincewa da yarjejeniyar tata.

Tsohon sakataren al'marin Brexit Dominic Raab ya ce ya yi amanna har yanzu cewa akwai yiwuwar samun wani sassauci daga EU kan yarjejeniyar Brexit, amma idan EU din ba ta sassauta ba, za a yi wata zazzafar tattaunawa kan ficewar ba tare da yarjejeniya.

Kuma mataimakin shugaban kungiyar 'yan majalisa 'yan ba ruwana Steve Baker, ya ce zai iya yin murabus a matsayin mai tsawatarwa na jam'iyyar Conservative, a kan ya kada kuri'ar amincewa da yarjejeniyar.

Mene ne mataki na gaba?

Idan ba a amince da yarjejeniyar Mrs May ba a wannan makon, to da alama 'yan malajisa za su koma tattaunawa kan wasu zabukan da aka yi watsi da su ta hanyar bin matakin kada kudi'a.

Sau biyu 'yan majalisa sun yin watsi da kudurin nata: a watan Janairu da kuri'a 230 - kuri'a mafi yawan da aka taba kadawa don adawa da wani kuduri na gwamnati mai ci a tarihin kasar - sannan a watan Maris kuma aka kayar da kudurin nata da kuri'a 149.